Connect with us

TATTAUNAWA

Tattaunawa Ta Musamman Da Wazirin Zazzau Alhaji Ibrahim Muhammad Amin

Published

on

Masanin Kididdigar kudi -Basarake -Manomi -Mai tallafa wa al’umma
Wakilinmu da ke Zariya a jihar Kaduna, BALARABE ABDULLAHI, ya sami damar zantawa da mai girma WAZIRIN ZAZZAU, ALHAJI IBRAHIM MUHAMMAD AMIN, inda ya bayyana ma na tarihinsa dalla-daklla, ba tare da yin jibge ba. Mai girma Wazirin Zazzau
ya fara da bayyana wa wakilinmu inda aka haife shi ya zuwa matsayin wazirn Zazzau day a ke kai a yau.

Za mu so ka fara bayyana ma na inda aka haife ka.
An haife ni a watan 19 ga watan Maris na shekara ta 1948, a wani kauye da ake kirarsa Gangara ta karamar hukumar Giwa a yau, amma wancan lokaci, karamar hukumar Zariya ne. Na fara karatun addinin musulunci, wato karatun Allo, bayan na sami ilimin addinin musulunci mai yawa, sai aka sa ni a makarantar firamare, a makarantar farko a birnin Zariya (Town School Number One), wadda ake kirar tad a sunan Waziri Lawal a yawai, na sami shiga wannan makaranta a shekara ta 1956, saboda canjin aiki da aka yi wa baba na, sai a shekara ta 1961, bayan nada baba na Sa’in Zazzau, hakimin Chukun a wancan lokaci, sai aka cire ni a makarantar da na`bayyana, zuwa Kujama na ci gaba da karatu na a can,mun hadu da wasu da mu ka ci gaba da karatu tare da su a wannan makaranta da ke Kujama,a shekara ta 1963 kuma sai aka da` baba na Zariya na kammala karatun firamare na a Zariya, a makarantar da na farad a na bayyana a baya. Ina kammala firamare, sai na sami shiga makarantar koyon aikin akawu da kasuwanci (Commercial Collage Zaria), amma a lokacin da na shiga tan a makaranta ce bat a gwamnati ba, wanda ya mallaki wannan makaranta shi ne Mista Dawotola, kuma ba zan manta ba, a na biyan kudin makaranta ne ta yawan darussan da dalibi ke nazari a makarantar.A lokacin da na fara karatu a makarantar zan iya tunawa a kwai darussan kasuwanci da kuma na Sana’o’i.sai kuma darussan da suke da alaka da mulki.

A lokacin wani bangare na darasi ka zaba?
Ni a lokacin na zabi bangaren lissafi da kuma kididdiga, zan iya tunawa a cikin darussan da na dauka a kwai darasin buga keken rubutu, wato tafureta, a shekara ta 1969, mai aiki da tafureta na karamar hukumar zariya ya bari, sai aka fara neman wanda ya iya wannan keke a lokacin Baba na na matsayin babban dan majalisar Sarkin zazzau Alhaji Muhammadu Aminu, wato wazirin Zazzau, sai ya tura ni a gwada ni ko zan iya aiki da wannan keken rubutu, daga gwaji, sai aka ga na iya aiki da keken, sai aka dauke aikia karamar hukumar Zariya (natibe
Althority). Kuma na fara aiki a matsayin ana biya na ladar aikin da na yi a kullum a lokacin ana ba ni Sule shida da kwabo shida.A karshen wata za ka na sami, da ya ke a wancan lokaci, ana hutun aiki a ranar Lahadi ne, wato ana aiki a ranar Asabar, sai ka ga ka tashi da naira goma sha hudu zuwa sha biyar. A shekarar 1970, aka yi ma ni canjin aiki daga inda na bayyana a baya zuwa ofishin Birnin da Kewaye, a matsayin mai buga keken Tafureta kuma karamin magatakarda a wancan lokaci, kuma a wancan lokaci,Alhaji Abdulrahman Dikko, mahaifin marigayi Dkta Umaru Dikko shi ne Hakimin Birnin da kewaye, na yi aiki a wannan ofishi har zuwa shekara ta 1971 zuwa 1972, aka tura ni na yi karatu a Kaduna a (federal training
Centre) da ke Kaduna, na yi kwas kan aikin babban akawu,a shekara ta 1972, da na dawo daga wannan kwas na ci gaba da aiki, har dai zuwa 1973, a wannan shekara ne Alhaji Abdulrahman Dikko ya aje aiki, a matsayin hakimin birni da kewaye, sai Allah cikin ikonsa, Sarkin Zazzau na yanzu, ya na wakilin ofis, sai aka nada shi Dan madamin Zazzau,sai aka ba shi kujerar Hakimin birni da kewaye a shekara ta 1975.

Kun zauna da shi kenan tun ya na Dan Madamin Zazzau?
Babu ko shakka wannan batu haka ya ke, mu na tare tun daga lokacin da a ka nada shi Dan madamin Zazzau ya zuwa shekara ta 1975 da Allah ya tabbatar ma sa da kujerar masarautar Zazzau a shekara ta 1975. Bayan Dan madamin zazzau ya zama sarkin zazzau, sai nag a baa bin da ya dace in yi sai ko ma in ci gaba da karatu, sai na koma kwalejin kimiyya da fasaha ta Kaduna (Kadpoly), na sami takardar shaida kan aikin da na ke yi, da na kammala,sai na dawo na ci gaba da yin aikin da aka dora ni a kai.A shekarar 1976, aka kirkiro kananan hukumomi a wannan lokaci duk mu na wajen karatu, duk ma’aikata kuma aka tura su kananan hukumomi, kuma zan iya tunawa karamar hukumar Zariya, ba ta da ma’aikata, musamman ma dai bangaren kudi da kuma bangaren baitul-mali, a wannan likaci, Katukan Zazzau na yanzu Alhaji Isyaku Suleman, shi ne Ma’ajin karamar hukumar Zariya, da na dawo na sami ba shi da ma’aikata,da nay a ganni sai ya tambaye ni, ina ina? Sai na ce ma sa yanzu na dawo daga karatu, sai ya`ce me na karanta? Na ce ma yi ma sa bayanin abin da na karanta, sai ya ce in dawo Baitul-malin karamar hukumar Zariya, nan na ci gaba da aiki a matsayin mataimakin jami’in da ke kula da kudi, har dai zuwa 1977, sai aka kafa kwamitin tantance kayayyakin kananan hukumomi , sai aka sa shi ma’aji ya kasance a cikin wannan kwamiti,sai ya ce ba zai sami zuwa aiki a cikin wannan kwamiti ba, amma in an yadda a kwai mataimakinsa, zai wakilce shi a wannan kwamiti, aka yadda da bukatarsa, ya tura ni, na shiga wannan kwamiti,nak shiga cikin mutum tara da suke cikin wannan kwamiti, a karkashin jagorancin marigayi Alhaji Ibrahim Kankara, wannan bawan Allah shi ne babban jami’in da ke kula da lafiyar al’umma ta jihar Kaduna, babban mai binciken kudi na jihar Kaduna Alhaji Dalhatu Bello, duk suna cikin wannan kwamiti.

Wata nawa ku ka yi ku na wannan aiki?
Mun yi wata bakawai, kuma ka tuna a lokacin mu na tare da Katsina ne, duk kananan hukumomin da suke lardin Zazzau da lardin Katsina duk mun je mun yi aikin da aka dora ma na, mun kuma kididdige kayayyakin da mu ka gani, domin raba wa gasabbin kananan hukumomin da aka kirkiro daga tsofaffin kananan hukumomin jihar Kaduna, bayan mun kammala aikin sai mu ka mika rahoto ga gwamnatin jihar Kaduna, sai na dawo wajen aiki na a` Zariya. Sai kuma a shekarar 1978, na sake koma wa kwaklejin kimiyya da fasaha ta jihar Kaduna,na sami shaidar karamar difiloma, a shekara ta 1980 kuma da na kammala wannan karatu, sai aka tura ni, karamar hukumar Funtuwa na yi sanin makaman aiki na karatun da na yi, na tsawon shekara guda,ina kammala sanin makaman aiki a Funtuwa, sai na kara koma wa wannan kwalejin inda na sami babbar difiloma a shekara ta 1981zuwa 1982.Ina kammalawa sai na dawo ofis na ci gaba da aiki har zuwa 1983,da aka yi zabe aka kirkiro kananan hukumomi ku san 70 a jihar Kaduna, bayan kammala zaben, sai aka nada ne Sakataren karamar hukumar Zariya a shekara ta 1983,bayan wata uku, aka sami matsala aka rushe kananan hukumomin, sai na ci gaba da aiki na har zuwa 1988, sai aka nada ni mai binciken kudi na karamar hukumar Zariya, bayan shekara daya ina kan wannan mukami, sai 1989, aka sake kirkiro kananan hukumomi,a karamar hukumar Kaciya, aka kirkiro zango da kuma cukun, ni na fara zama ma’ajin karamar hukumar Cukun, na zauna a cukun daga 1989 zuwa 1990,sai a 1990 aka sake kirkiro kananan hukumomi, sai aka raba karamar hukumar Soba da Sabon gari, daga Ikara na dawo Soba har zuwa 1994 sai aka mayar da ni Makarfi,daga makarfi sai aka tura ni Karamar hukumar Kaduna ta arewa, a shekara ta 1997, aka sake kirkiro kananan hukumomi, aka tura ni karamar kukmar Kubau,zuwa 1998, daga nan sai aka sake kai ni Kajuru, na zauna a kajuru har zuwa shekara ta 2000, a wannan shekara aka yi ma ni canjin aiki zuwa Karamar hukumar Birnin Gwari, na yi shekara uku, aka sake da ni karamar hukumar Sabon gari ban shekara a nan ba, sai aka mayar da ni karamar hukumar Jaba, na yi shekara daya da`watanni,daga Jaba, sai aka sake dawo da ni karamar hukumar Makarfi,a shekara ta 2007, na aje aiki, wato na yi ritaya daga aikin gwamnatin jihar Kaduna, kuma duk kananan hukumomin da na bayyana an tura ni aiki, na je ne a matsayin ma’ajin karamar hukuma.

Wasu matsaloli ka fuskanta saboda yawan canjin da aka yi ta yi maka?
Matsalolin da na fuskanta su ne, duk karamar hukumar da aka tura ni, sai in ga a kwai matsaloli a ayyukan da ake yi, da zarar na kammala gyara, sai a yi ma ni canji, duk kuma inda na je abubuwan da na ke gani ke nan, sai na fahimci gyara ake tura ni in yi, da zarar na kammala gyaran, sai in zura ido, na ganin takardar canji zuwa wata karamar hukumar, abubuwan da suka dunga faruwa ke nan a tsawon shekarun da na yi a aikin gwamnati.

Ka taba samun yabo a ayyukan da ka yi?
Lallai na sami takardar yabo da marigayi Alhaji Umaru Yeroson ya ba ni, a lokacin ya na matsayin mai binciken kudi na gwamnatin jihar Kaduna, inda y ace ya na yaba ma ni tare da godiya na yadda na ke aiki, ya ce, ya bi duk inda na yi aiki, abin da ya ke gani,gyara na ke yi, ya kara da cewar, bai ga inda aka kai ni, ya ga waje ne mai kyau ba.wannan takarda ta kara ma ni kkarin gwiwa na tsawon lokutan da na yi ina aikin gwamnati ya zuwa yau.

Ya ya ka ke yin gyaran da ka yi?
Ai duk matsalolin da na samu a duk karamar hukumar da aka tura ni, da ma’aikata ma ke taruwa, in jagorance su ma yi gyaran, shi ya sad a zarar an ce zan tashi, sais u nuna damuwarsu.

Wace alaka ka ke kullawa a tsakaninka da ma’aikatan da ka samu ko ka hadu da su?
Ai ni duk inda na je ina daukar ma’aikaci abokin aiki ne, das u kuma na ke hada hannu mu yi duk gyare-gyaren da suka dace.Kuma nuna ma su mu tsaya mu rike amanar aikin mu kuma san yadda za mu yi aikin.

A karshe wani sako ka ke da shi ga ma’aikata a yau?
Babban sakon shi ne, su rungumi ayyukansu da hannu biyu, tare da yin ko wane aiki tsakani da Allah tare kuma da rike amanar da aka dora ma su, in sun yi haka sais u fara lafiya, su kuma kammala lafiya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!