Yadda A Ka Yabawa Gwamna Ganduje A Taron NCM — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

RAHOTANNI

Yadda A Ka Yabawa Gwamna Ganduje A Taron NCM

Published

on


Taron National Council Meting karo na 61 wanda akeyi duk shekara a sassa daban daban na Jahohin Kasan nan akan harkar bunkasa Lafiya wanda Jahar Kano ta karbi bakuncinsa a Bana karkashin Jagorancin kwamishinan Lafiya Dr. Kabiru Ibrahim Getso taron na bana wanda ya samu halartar daukaci ko mafiya yawa na Kwamishinonin Lafiya na Kasa ko wakilansu anyi shine a dakin Taro na Gidan Gwamnatin Kano.
Daga cikin jawabai da ra’ayoyi na Kwamishinonin Lafiya na Jahohi sun bayyana tsare tsaren da suke aiwatarwa a Jahohinsu akan harkar lafiya da kuma yadda suka yabawa Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje akan yadda ya shiryawa Taron shatara ra arziki da kuma yadda Gwamnan yayi fice wajan bunkasa harkar lafiya da sauran cigaba ga al’ummar Kano baki daya a kowanna fanni na rayuwa.
Dr. Mustapha Jibrin shine Kwamishinan lafiya na Jahar Niger ya bayyana cewa hakika Jahar Niger bisa goyan bayan Gwamna Abubakar Sani Bello lafiya ta samu kulawa da tagomashi a Jahar Niger wanda yanzu Niger takai kimanin kashi 13 na kasafin kudi akan harkar lafiya.
Shi ma Dr. Muhammed Bello Kwamishinan Lafiya na Jahar Yobe ya bayyana cewa Jahar Yobe ta haura kashi 15 cikin dari na abinda zata kashe a harkar lafiya na kasafin kudnta na shekara wanda kasha 15 shi ne kololuwa na Yarjejeniyar Abuja Declaration wanda shi ne akace Jahohi suyi kokarin kai haka to ita Jahar Yobe ta haurama haka acewar Dr. Muhammed Bello Kwamishinan Lafiya na Jahar Yobe.
Shi ma Dr. Balarabe Kakale Shuni Kwamishinan lafiya na Jahar Sokoto ya ce yadda Gwamna Aminu Waziri Tabbuwal ya bawa mahimmanci shi ne akasa mu harkar cgabanlafiya a Sokoto dan haka ne yanzu Jahar Sokoto take da tare tsare na bunkasa harkar lafiya da kuma yaki da harakar Shan Miyagun Kwayoyi da kuma warkar da wadanda suka samu kansu a matsala daga cikin Matasa da saran su.
Haka kuma a karshe Kwamishinonin Lafiya na Kudu, Arewa, Gabas da Yamma na Kasan nan da suka halarci Taron sun yabawa Gwamna Ganduje akan Aiyukan cigaban Kano kamar yadda Kwamisinan Lafiya na Kano Dr. Kabiru Ibrahim Getso ya bayyana farin cikin sa akan Ayukan Gwamnan Kano da kuma yadda Taron NCM na 61 ya samu Nasara.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!