Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yar Aiki Ta Maka Sanata A Kotu Bisa Zargin Dirka Mata Ciki

Published

on

Wata ‘yar aiki mai suna Winifred ta maka Sanata Kimani Wamatangi a kotu à bisa zargin dirka mata ciki tare da kuma yin watsi da ita da abin da ta haifa masa yar shekara goma ba tare da yin aure ba.
A cewar Winfred Wangi, sanatan sau biyu kacal yazo ya ganta da yarinyar data haifa masa a lokacin yarinyar tana da watanni biyu da haihuwa,inda ya bani dala 69.37 karshen shekarar 2017 a lokacin da ya sake tsayawa takara majakisar kasar Kenya.
Ta ci gaba da cewa, ya kuma yi ikirarin cewar yazo yaga mahaifiya ta a gida inda yace wai ya bata dala198.20 don kula da yarinyar kuma ya yi alkawarin zai ci gaba da baiwa yarinyar kulawa.
Ta bayyana cewar, tun lokacin data haifi yarinyar a ranar 23 ga watan Afirilun 2007, Wamatangi ya kawai tura mata dala 693 ce.
A takardar rantsuwa ta sanatan da lauya mai kare shi ya karanta a gaban kotu ya bayyana cewar akwai matsala a kan sanatan in har ya amince zai dinga baiwa yarinyar kula ta hanyar biya mata kudin makaranta dala 148.65 da kudin gidan haya da kuma dbiyan dala 198.20 don à dinga duba lafiyar ta da sittira da sauran matsalolin ta ba.
Matar ta kuma sanarwa da kotun cewar, Wamatangi har yanzu bai je an dauki jinin sa ba don tantancewa duk cewar kotu ta bayar da umarnin ayi hakan.
A wasikar da maaikatar kiwon lafiya ta gabatarwa da kotun bin hakkin yara ta kasar wadda jamiar gwamnatin kasar AW Nderitu ta sanyawa Jenny ta ce, wannan alamu dake nuna cewar. Winfred Wangui Kimani ta gabatar da kanta ga gwamnati a ranar 28 ga watan Mayu da karfe 9:30 na safiyar ranar don ayi mata gwajin jini, amma kuma baza a iya samun cikakken sakamako ba saboda Paul Kimani Njoroge yaki kawo kansa don shima a dauki nasa jinin don ayi gwajin.
A cewar Wangui ta maka sanatan a kotu tun cikin shekarar 2014, amma lauyoyi sunyi watsi da shariar ta,ibda hakan ya janyo ba cewar fiyil dinta na karar
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: