Connect with us

RA'AYINMU

Matakin Soke Karatun HND Alheri Ne

Published

on

A kwanakin baya ne gwamnatin tarayya ta soke ba da takardar shaidar karatun Babban Difiloma (HND) da makarantun kimiyya da fasaha (Polytechnics) ke bayarwa. Matakin wanda Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta dauka lokacin da take taronta na mako-mako, ya raba gardama kan ja-in-jan da ake yi a kan fifita takardar shaidar karatun Digiri da ta HND.
Wannan ya yi kyau kwarai da gaske, majalisar zartarwar ta tarayya ba ta dauki matakin ba sai da ta yi garambawul game da tsarin manyan makarantun kasar nan. Yanzu haka, ba za a kara baiwa wani takardar shaidar karatun na HND ba, baya ga wadanda suke nazarin matakin karatun a halin yanzu. Bayan haka, duk wani karatu da makarantun kimiyya da fasaha ke koyarwa da suka yi hannun riga da kimiyya da kere-kere su ma an soke su. Sabon matakin ya nunar da cewa makarantun kimiyya da fasahar za a mayar da su harabobin jami’o’i mafi kusa da su, inda mataimakan shugabannin jami’o’i za su rika nada shugabanninsu.
Domin fara aiki da sabon tsarin, biyu daga cikin fitattun makarantun kimiyya da fasahar, ta Kaduna da ta Yaba, za a rika kiransu da Jami’o’in Fasaha na cikin birni. Daga yanzu an takaita ikon makarantun ga bayar da shaidar karatun Difiloma ta kasa (ND) kawai, sannan daliban da suka kammala a cikinsu idan suna da muradin cigaba da karatunsu na digiri, za su yi hakan amma wata jami’a ce mafi kusa da wadannan makarantun za su ba su takardar shaidar digirin bayan sun kammala. Majalisar zartarwar ta tarayya ta kuma amince da gabatar da kudirin dokar sabon tsarin guda biyu ga majalisun dokoki na kasa domin tabbatar da su. Kudirin doka na farko ya kunshi shirye-shiryen mayar da makarantun kimiyya da fasahar nan biyu jami’o’i, kana na biyun yana neman cigaba da shirin mayar da dukkan makarantun kimiyya da fasaha da kwalejojin ilimi na gwamnatin tarayya su zama harabobin jami’o’i mafi kusa da su.
Babu mamaki wani ya ce ai tun fil’azal an kafa makarantun kimiyya da fasaha ne domin tabbatar da bunkasar fasaha da kere-kere a kasa, haka batun yake, amma kuma kar a manta da cewa darajar ilimi a wadannan makarantun ta yi muguwar faduwa fiye da ta jami’o’i. Bugu da kari, batun da ake yi cewa darajar ilimin ta fadi ce a dukkan matakan ilimi na kasa, manuniya ce ga gwamnati ta dauki dukkan matakan da suka wajaba wajen farfado da darajar ilimin. Damuwar da wasu ke nunawa ta yadda a ganinsu sabon tsarin zai iya karya lagon ilimin fasaha da kere-kere a Nijeriya; an magance ta bisa la’akari da cewa idan aka dauki kwararan matakan inganta ilimin fasaha, hade makarantun kimiyya da fasaha da jami’o’i zai taimaka a samar da isassun kwararrun ma’aikatan da masana’antun kasar nan suke bukata. Har ila yau, ana sa ran cewa sabon tsarin zai rage yawan dogaron da ake yi da ma’aikatan da ke zuwa daga kasashen waje wurin bunkasa cigaban masana’antunmu tare da habaka fasahar kirkira a cikin gida da bullo da sabbin abubuwan da za ci gajiyarsu ta fannin fasaha.
A ra’ayinmu, wannan sabon matakin na gwamnati a kan tsarin ilimin kimiyya da fasaha a kasar nan shi ne mafi dacewa, ganin yadda sha’anin bayar da takardun gurbin karatu a makarantun kimiyya da fasaha yake kwan-gaba-kwan-baya tun daga shekarar 2010, a sakamakon halin-ko-in-kula da gwamnati ta nuna wajen bunkasa ilimin fasaha da kere-kere a kwalejoji da manyan makarantun kimiyya da fasaha.
Wakazalika, matakin da aka dauka a sabon tsarin na takaita bayar da shaidar karatun HND ga daliban da suke kan matakin karatun a yanzu haka; abin a yaba ne, da kuma yadda aka soke duk wani karatu da ba shi da alaka da fasaha da kere-kere a makarantun kimiyya da fasahar wanda ya kai kashi 70 a cikin 100 na yawan kwasa-kwasan da makarantun ke yi. Daga bayanan da muka samu, Nijeriya tana da makarantun kimiyya da fasaha sama da 112 ciki har da na tarayya guda 27, na jihohi 41 sannan masu zaman kansu mallakar daidaikun mutane guda 44.
Akwai wasu da ke zullumin cewa jami’o’in da ake da su ba za su iya daukar adadin makarantun kimiyya da fasahar da ake da su ba wanda ake wa kallon madogarar daliban da ba su da kwazon samun makin shiga jami’a.
Masu wannan tunanin su kwantar da hankulansu, domin idan aka lura da cewa Nijeriya mai yawan jami’o’i 153 da ke iya daukar dalibai kimanin milyan 150, za su iya karbar adadin daliban da ke son cigaba da karatu a wurinsu daga makarantun kimiyya da fasaha. Bayanai game da jami’o’in Nijeriya na nuna cewa akwai jami’o’in gwamnatin tarayya guda 40, da na gwamnatocin jihohi 44 da kuma masu zaman kansu 74 wanda idan aka hada jimillarsu sun cika 153. Idan aka kara da yawan karin jami’o’i 200 da a yanzu haka Hukumar Jami’o’i ta Kasa ke tantancewa, adadinsu ya kai 353. Wannan ya nuna cewa muna da isassun jami’o’in da za su toshe gibin da za a samu na karancin jami’o’i a Nijeriya.
Baya ga kasancewar sabon tsarin na manyan makarantu abin lale marhabin bisa yadda zai shawo kan matsalar faduwar darajar ilimi a makarantun kimiyya da fasaha, har ila yau zai zama mataki na farko wajen cike gibin da aka samu na karatu a tsakanin matakan manyan makarantu a kasar nan. Sannan ya kamata al’umma su daina kallon daliban da ke karatu a makarantun kimiyya da fasaha a matsayin wadanda ba su da kwazon zuwa jami’a, domin galibin wadannan daliban sun cancanci shiga jami’a, illa rashin samun gurbin karatu a jami’ar ne yake kawo musu cikas.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!