2019: An Gudanar Da Gangamin Nuna Goyon Bayan Buhari Da Osinbajo A Kaduna — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

2019: An Gudanar Da Gangamin Nuna Goyon Bayan Buhari Da Osinbajo A Kaduna

Published

on


Kungiyar Matasan ‘Yan Majalisu dake yankin Arewa maso Yamma masu nuna goyon bayansu ga Buhari da Osibanjo, sun gudanar da taron gangamin nuna goyon bayansu ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Da Mataimakinsa Osibanjo, domin ganin sun amince sun sake tsayawa takarar Shugabancin Kasar nan a karo na biyu.

Taron wanda ya gudana a Sakatariyar ofishin Kungiyar dake kusa da Kofar Gamji gate, dake Kaduna, ya sami halartar dimbin Matasan ‘Yan majalisu dake shiyyar Arewa maso yamma, wanda suka hada da Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto, Sokoto da kuma Jihar Zamfara.

A yayin da yake Jawabi a matsayinsa na babban bako wanda ya wakilci Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawal, wanda Sanata Habu Ibrahim, ya wakilta, ya bayyana wannan taron kungiyar  Matasan ‘Yan majalisu na Yankin Arewa maso Yamma, masu nuna goyon bayansu ga Buhari da Osibanjo, a matsayin wani babban shimfidar samun nasarar sake tafiyar Shugaban kasa Buhari da Osibanjo a zango na biyu, domin a cewarsa, tun da har matasa da kansu sun yarda sun amince da salon tafiyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, to lalle ko shakka babu Buhari ya gama cin zabe, sai dai jiran lokacin rantsarwa kawai.

Sanata Habu Ibrahim, ya kuma kara da jinjina ma wadannan Matasan ‘Yan majalisu wanda ya kira su da sunan fitilar tafiyar Buhari da Osibanjo a zangon na  biyu, a matsayin Matasa masu kishin kasar su, wadanda suka ki yarda wasu batagarin ‘yan siyasa marasa kishin Arewa, masu yiwa wannan gwamnati zagon kasa suyi amfani da su, wajen ganin an gurgunta salon tafiyar alheri na Shugaba Buhari ga ‘yan Nijeriya.

Shima a nasa jawabin a wajen taron Matasan, Sanata Adamu Aleru daga Jihar Kebbi, ya bayyana wannan tafiya da wadannan matasa suka dauko a matsayin abin a yaba masu ne, musamman a dai dai irin wannan lokaci da kasar ke neman goyon bayan matasa masu kishin kasa wadanda zasu fito su sadaukar da kansu wajen marawa Shugaba Buhari baya domin ganin ya ci gaba da fafutukar aikin alkhairi da ya dauko yi ma daukacin yankin Nijeriya baki daya, ba tare da nuna kabilanci ko banbancin addini ba.

Sanata Adamu Aleru, ya ce, Shugaba Buhari mutum ne jajirta ce wanda sam bai damu da kwkdayin abin duniya ba, shi dai kullum burinsa bai wuce na ganin ya dawo da martabar da kuma kimar kasar nan a idon duniya, musamman a lokutan baya da kasar nan tayi kaurin suna wajen cin hanci da rashawa a idon duniya, wanda a dalilin hakan ne kasar ta sami mummunar koma baya ta fuskar karyewar tattalin arzikin kasa, matsalar rashin tsaro da dai sauran su.

Tun da farko da yake jawabin maraba, Shugaban Kungiyar, wanda kuma shi ne Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Honarabul Aliyu Sabiu Maduru, ya bayyana cewa, sun kirkiro da wannan kungiya ne domin ci gaba da nuna goyon bayansu dari bisa dari ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, da kuma kara fadakar da Al’ummar kasar nan irin dimbin ayyukan alkhairin da Shugaban kasa Buhari ya kawo ma ‘yan Nijeriya, da kuma wanda zai kawo nan gaba idan ‘yan Nijeriya suka yarda, Allah ya sake dawowa da shi Shugabancin kasar nan a karo na biyu.

Honarabul Aliyu Maduru, ya kuma kara yin roko musamman ga daukacin Matasan Arewa da cewa, lokaci ya yi wanda za su fito kwansu da kwarkwatansu domin sake nuna goyon bayansu ga Shugaban kasa Buhari domin ganin ya sake darewa kujerar mulkin kasar nan idan Allah ya kaimu shekara ta 2019 mai zuwa.

Daga karshe, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, ya godewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a bisa yadda ya yarda ya amince ya sanyawa dokar da ta baiwa duk wani Mashi damar tsaya takarar kowace kujerar siyasar kasar nan, ba tare da maganar karancin shekaru ba, a cewarsa, wannan ba karamin abin a yaba ma Shugaban kasar ba ne

Taron dai ya sami halartar dimbin ‘yan majalisar dokokin jiha, da kuma na Tarayya, shahararrun mawakar jam’iyyar APC, irin su Dauda Kahutu Rarara, da dai sauran su.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!