Connect with us

LABARAI

An Tsinci Gawar Diyar Tsohon Mataimakin Gwamna A Dakin Saurayinta

Published

on

An tsinci gawar diyar tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo, Alhaji Lasisi Oluboyo, a dakin saurayinta a garin Akure babban birnin jihar Ondo.

Marigayyiyar mai suna, Adeola Khadijat Oluboyo, tana matakin ‘Lebel III” a jami’ar Adekunle Ajasin dake Akungba-Akoko, ta bace ne a makon daya wuce, da farko anyi zargn cewa ta hada hannun masu garkuwa da mutane ne.

Daga baya ne aka tsinci gawar Adebayo a dakin saurayinta jiya inda nan take jami’an ‘yan sanda suka cafke saurayin  nata.

Maiyarmu wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana wa wakilinmu cewa, wanda ake zargin bai dade da dawo wa daga kasashen waje ba, ya kuma yanyankata ne ya kuma kwashe wasu muhimman bangarori daga sassan jikinta, daga dukkan alamu don yin tsafi.

Jami’in watsa labaran rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, Femi Joseph, ya tabbatra da gano gawar da kuma cafke saurayin yarinyar, ya ce, ‘yan sanda sun yi mako daya suna neman yarinyar, tun lokacin da aka bayar da rahoton bacewarta.

Ya ce, saurayin yarinyar har ya birne gawar yarinyar, daga baya ne aka tono gawar daga ramin daya turbudeta.

Ya kara da cewa, za a gabatar da wanda ake zargin a gaban ‘yan jarida nan da awanni 24 inda ‘yan sanda zasu yi karin bayani a kan yadda lamarin ya kasance.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!