Baragurbi Ke Haifar Wa Da Gwamnatin Buhari Cikas (II) –Dakta Bature — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Baragurbi Ke Haifar Wa Da Gwamnatin Buhari Cikas (II) –Dakta Bature

Published

on


Kuma idan ka dauki Amurka ta Arewa wato ‘Latin’ ai su ma fiye da kashi 70 ai rayuwar da suke yi bai ma kai dala dayar ba. ina ga ba a san irin rayuwar da suke ba, rauwar wadanda suke birane kawai ake gani, ka ga dauki ‘Carabian Island’ su ma bai fi kasa biyu ko uku da za ka ce ainihin suna rayuwa sama ma da dala daya ba. Sabida haka kuma idan dauki kasashen nan na Magarib koda yake na fada suna cikin Afirka, su ma irin wannan rayuwar ta Nijriya sun fi sau dari bisa dari.

Haka kuma idan ka duba kasashen Asiya ga su irinsu Burma din nan, irinsu Betnam, ga su nan dai da yawa kasashe fiye da rabinsu ga su nan haka suke rayuwa ta talaci. To ai mu ba ma rayuwar talauci, kuma idan ma muna rayuwar talaucin ma su wa ye suka jefa a talaucin? Ai wadanda suka jefa mu a talaucin ai da su za a yi kuka, don su suka talauta mu suka talauta kasar ta mu, suka mayar da mu baya.

A takaice zantuttuka irin wadannan da suke fitowa na Bankin duniya ne, kuma na kungiyoyi ne na turawan nan, to da yawa kungiyoyin da suke kasashen nan ma kudi ake bas u su kirikiri zance su watsa shi akan kasarmu Nijeriya, ko a kan gwamnatin kasarmu, ko akan Shugaban kasarmu, su yarfa shi saboda ana son a juya hankali talakawa. Idan ka juya hankalin talakawa ka birkita kasar, wa za ka dora wanda zai daidaita ta, wa za ka dora wanda sai ya koma kasa ya faro gininta, wa za ka dora  wanda ma yake da niyyar ginin?

Me za ka ce game da wadanda ke kawo wa wannan gwamnati Cikas?

Su wadannan da suke ta yi wa wannan tafiya ta wannan gwamnati cakulkuli, mutane ne wadanda suke ‘yan ta kife ne kowa ya rasa, domin sun riga sun tanadi abubuwan da suka sata da su da ‘ya’yansu. Saboda dan Nijeriya idan kana daka ta tasu, suna da yadda za su yi, suna da fukafukin tashi, in kasar ta dame su ma ai tashi za su yi su bar kasar su tafi su ci dukiyar da suka tara, ko yanzu haka da yawa ‘ya’yansu ba sa kasar, da yawansu ba za su yi wata ba sai sun fita wajen kasar.

Amma kai dan Nijeriya da za ka yi addu’a kasarka ta kyautata, kasarka ta kintsu, kasarka ta rayu, in Allahu Rabbi a dawo a yi sabuwar rayuwa wacce muke tsammani, ya kamata ace ka ba da gudunmawa da hadin kai da goyon baya, ba wadanda suke son su samu milkin Nijeriya bas u sake mayar da ita baya, ta koma hannu wadanda ba su da tsari na gyaranta, tunaninsu kawai ya za a yi su samu wata kofa da za su yi facaka su da wadanda suke so, su sha abin da suke so su sha, su ci abin da suke so su ci. Kai kuma da ake ta zugawa kana ganin laifin Shugabanni, ai duk abin da ka ga ba a samu ba to hakuri ne babu, kuma duk abin da hakuri bai yi ba, to rashin hakurin ma ba za yi ba. Kuma duk abin da ainihin ka ga ana ta gaggawa a cikinsa, to fa addini ya nuna gaggawa shaidan ne a cikinta, jinkiri kuma daga Allah ne. saboda haka wannan jinkiri da a kai yanzu mutane ba su ga abu ya haska ba, to wallahi abin yana gab da ya haska, na tabbata in za a ba wa wannan gwamnati damar sake komawa zango na biyu, to tun shekararta ta farko za ka ga duk abubuwan da suke damun ‘yan Nijeriya birni da kauye kusan sun fara zama tarihi.

Wato wadannan mutane suna zaton da Buhari ya ci mulki zai ba su dama su yi sace-sace, su yi sharholiya, su yi son zuciya. Ko kuma ya barsu bai bincike su ba, don haka suka bar shi ya dawo, kuma duk kokarin da za su yi su hana shi dawowa dan Nijeriya a gabanka a ka yi ta tade shi. To alkawari ne na Allah, Allah ya nufa sai ya yi, kuma Allah ya riga ya rubuta masa ceton Nijeriya ga ‘yan Nijeriya in Allah ya so ya yarda ta wajensa zai bullo.

Saboda haka mu mara masa baya, mu bishi da addu’a mu bishi da shawarwari masu kyau, mu rika ba da shawrwarinmu a rubuce, na tabbata in muna turawa ta hanyar da shawarwarin nan za su same shi, na tabbata in wata shawarar bata yi aiki ba wata za ta yi. saboda haka Shugabanni ba a kushe su, ba a la’antarsu, duk Shugaban da ka sani Musulunci yana zaginsa, kar ka kushe shi kada ka la’ance shi. In dai aka ce ya riga ya zama Shugabanka musamman shugabanci irin na zamanin nan mai iyaka-iyaka, to biye masa iya iyakar da zaiyi mulki. Sai ka addu’ar da zai zama dai-dai, kai ma watakila kai ma ka ga dai-dai din, in kuma kana zagin Shugaba kana tsine masa, to fa lalacewar ta samu kasarku, an riga an yanka masa zangon da zai yi kuma yayi.

Ta wacce fuska ne manoma suka ci gajiyar wannan gwamnati?

Ai mu ’yan Nijeriya Allah ne ya yi mana zabi, zabin wannan bawan Allah, mu yi hakuri, ka ga misali manoma, ai ka ga irin tsarin da ake tallafa masu da taki a baya a shekarar 2016 da 2017, to Shugaban kasa ya ga wannan tsari ya tsugunna da yawa, sai aka sake tsari shi ne, za a je a auna gonarka ko ta kai fadin Hekta 1000 Shugaban kasa ya ba da damar a baka taimako da-dai da Hektarka, in taka Hekta daya ce ko abin da ya kasa haka, Shugaban kasa ya ba da damar a baka taimako daidai da Hektarka.

To dan Nijeriya me kake so? Mu dai noman nan da kasuwanci dai dai su muka gada, wanda ya zo ya raya noma, ya karfafa guiwar manoma, ya ma hana cewar gwamnatocin jihohi su yi mu’amala da takin nan  aka ba da taki kai tsaye ga kungiyoyin manoma musamman AFAN ta kasa ko kuma ta Jihohi, za ka je ka yi rijista an ma hana a sa hannun gwamnoni, saboda in abin a hannunsu yake wanda suke so kawai suke ba wa wato wanda ke bin jam’iyyarsu, kuma gwamnatin Nijeriya gwamnatin kowa ce, wannan ita ce ka’ida, karamin manomi ko babban manomi zai kai takardunsa idan aka ga ya cika ka’idojin dai-dai za a ba shi abin da yake so.

Ba wai sai taki ba, ba wai sai nom aba, a a ko kiwo ko kuma abin da ya shafi amfanin gona, an ba da dama an fitar da kungiyoyin kudi, saboda haka ‘yan Nijeriya musamman ‘yan Arewa ko kuma ‘yan Nijeriya gaba daya, mu yi kokarin sanin hanyoyin da ake cin wannan gajiya, ana cin wannan gajiya ga manomi shi kadai, kuma ana ci ga kungiyoyoin manoma.

Idan kuna kusa ko ma a nesa kuke kuka nemi ofishin AFAN, ainihin ita ce babbar kungiyar, a takaice za a baku ka’idoji in kun cike a baku wannan abu. Ku kuma  mutanen AFAN, idan mutane sun zo ba su san yadda ake abin nan ba, musamman mutanen karkara in sun zo, ku ware mutanen da za su ba su bita ta yadda za su wayar da su yadda za su bi ka’idojin, kada ku dinga tsanar su kuna tsangwamar su, kuna korar su. To ai gabaki dayanmu ‘yan Nijeriya ne, kuma saboda mu Shugaban kasa ya saki wannan garabasa, musamman mutanen karkara da lunguna su ne abubuwa ba sa samunsu.

Ku ma’aikatan banki na kasa wato CBN da kungiyoyin manoma duk mutumin da ya zo ya cika ka’idoji, to ku ba shi dama ya ci amfanin wannan abu da aka fito da shi.

Daga karshe wane kira ka ke da shi ga ‘yan Nijeriya?

Muna addu’a ga Nijeriyam Allah ya daidaita ta, Allah ya mayar da ita kasa, kuma muna addu’a Nijeriyarmu mai albarkkoki da yawa Allah ya ci gaba fito mana da albarka mai yawa ta karkashin wannan Shugaba mai gaskiya.

Saboda haka lallai ne wanda aka ga zai zama hadari ga kasa, aka ga bai da kishin kasa, kokarinsa kawai ya haddasa fitina a kasa, lalai a tashi tsaye a yi maganinsa. Saboda haka da wannan nake takaitawa, kuma nake addu’a ga kamfaninku na LEADERSHIP bangaren turanci da Hausa, yadda kuke gamsar da mutane masu karanta jaridunku , da kuma kokarinku dakile abin duk da zai zama rigima a kasa, kuna ba da gudunmawarku gwargwadon iko, Allah yayi wa wannan kamfani naku albarka.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!