Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

‘Don Na Burge Matata Na Shiga Fashi Da Makami’

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja da kama wasu mutum biyu da ake zarginsu da aikata laifin fashi da makami, wadanda suka tare motocin da suka dauko kaya daga kasuwar Kokongi ta karamar hukumar Borgu.

Wadanda ake zargin su ne, Jariri Chede, dan shekara 25, da Janya Shehu, dan shekara 20, wadanda  rundunar ‘yan sanda ta ofishin ‘yan sanda na New Bussa suka kama bayan sun yi wa Sunday Ishaya na kauyen Kokongi  fashin zunzurutun kudi da kuma wasu kadarori.

Sun yi masa fashin ne lokacin yake tuka mota zuwa Kokongi wanda ya bi ta Wawa, inda suka kwace masa Naira dubu saba’in da kuma waya wadda aka kiyasta kudinta Naira dubu talatin da bakwai.

Haka kuma ‘yan fashin sun kwace katan biyu na giya wadda aka kiyasta kudinta Naira dubu tara da kuma katan din gwangwanin shake shi kuma na Naira dubu biyu.

Majiyarmu ta shaida mana cewa, ‘yan fashin sun fito ne daga daji da bindiga da adduna inda suka afka masa suka yi masa fashi karshe suka bar shi cikin jini kwance.

Daya daga cikin ‘yan fashin mai suna Shehu, ya gayawa majiyarmu cewa, bai dade da yin aure ba, saboda haka ya shiga fashi da makami ne domin ya samu kudin da zai kawo wa matarsa ya burgeta.

“Ba na so in ga matata ta rasa komai; saboda haka zan iya yin komai domin in burgeta. Na yi mata alkawarin cewa, duk abin da zan yi, zan yi domin ta yi farin ciki.Sai me kuma don ‘yanda sun kama ni”.

“Ba na da na sani, domin ina sani na shiga fashi da makami, saboda haka babu dalilin da zai sa na yi da na sani, sai dai kawai tsakanina da Allah,”in ji shi.

Da aka tambaye shi ko ya yake ganin matar tasa da ‘yan uwansa za su ji da wannan labari, sai ya ce, na tabbatar da cewa, matata ba za ta ji dadi ba, amma na riga na aikata laifin, su kuwa iyayena ina ba su hakuri a kan hakan.”

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, Muhammad Abubakar, ya bayyana majiyar ta mu cewa. ‘yan sanda na nan na ci gaba da bincike, wanda da zarar sun gama za su mika wadanda ake zargin zuwa kotu don yi musu hukunci.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!