Connect with us

MANYAN LABARAI

Fallasar Faifen Muryar ‘Yan Madigo: Hukumar Hisba A Kano Ta Fara Bincike

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta bayyana cewa, a halin yanzu ta fara bincike a kan faifan rukoda dake yawo a kafafen sadarwa na intanet inda wasu ‘yan mata ‘yan madigo daga jihar Kano ke zage-zage tsakaninsu a kan zargin kwace wa daya daga cikinsu abokiyar harkarta.

Faifen muryar dake yawo a kafafen sadarwa na intanet yana bayyana inda wasu mata ke anfani da miyagun kalmomi wajen bayyana irin badala da mugun aikin da suka yi da juna. Lamarin ya kuma tayar da hankali tsakanin jami’an tsaro jihar.

Wakilinmu ya gano cewa, ‘yan matan dake wadannan maganganu a cikin faifan muryar dake yawo an tabbatar da cewa, yaran wasu manyan mutane ne a cikin jihar Kano.

A kan haka ne mataimakin shugaban hukumar Hisban ta jihar kano kuma shugaban sashin binciken kwakwaf na hukumar, Malam Idris Ibn-Umar, ya bayyana wa wata kafar watsa labarai na intanet mai suna ‘DAILY NIGERIAN’ cewa, bayan da wannan faifan ya shiga hannusu a makon daya wuce sun dukufa bincike don gano yadda lamarin yake.

Malam Ibn-Umar ya kara da cewa, binciken da ofishinsa keyi nada hadin gwiwa ne tare da sauran bangarorin jami’an tsaron kasa kuma ana samun nasara da haske a binciken da ake yi sosai.

Ya ce, hukumar ta samu wasu karin bayanai, amma a halin yanzu tana kara zufafa bincike.

“Mun samu faifan muna kuma gudanar da bincike tare da sauran hukumomin tsaro dake aiki a nan Kano, nan take muka fara binciken lokacin da jami’anmu daga bangaren sashinmu na sintiri suka kawo mana.

“Zamu ci gaba da gudanar da bincikenmu kuma duk wanda ke hannu a wanna lamarin zai dandana kudarsa don kuwa zamu gurfanar dashi gaba kotu.

“Bana son gaya maku dukkan halin da binciken namu ke ciki amma ina mai sanar daku cewa, muna samun gaggarumin nasara a binciken da muke gudanarwa.” Inji Malam Ibn-Umar said.

Ya kuma kara da cewa, hukumomin tsaro na iya kokarinsu don gano asalin faifan muryar da kuma bankado wadnda keda hannun a kan wannan badalar.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!