Hadakan ’Yan Takarar PDP Damarar Kwace Mulkin Bauchi Ne -Akuyam — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Hadakan ’Yan Takarar PDP Damarar Kwace Mulkin Bauchi Ne -Akuyam

Published

on


Shugaban jam’iyyar adawa ta PDP, Alhaji Hamza Kosha Akuyam ya bayyana cewar hada kai da ‘yan takarar kujerar gwamnan jihar Bauchi a karkashin lemar PDP suka yi babban nasarace da take kara haska musu hanyar nasarar kwace mulki cikin sauki a hanun jam’iyyar APC a jihar Bauchi.

Akuyam ya bayyana hakan ne a zantawarsa da ‘yan jarida jim kadan bayan kaddamar da kwamitin dattawa na jam’iyyar PDP a jihar Bauchi a karshen makon nan, ya bayyana cewar sun rigaya sun kammala tsara yadda za su kwace mulki daga hanun jam’iyyar APC a jihar Bauchi cikin sauki.

Hamza Akuyam ya kara da cewa, idan suka yi la’akari da rashin cika alkawura da APC ta yi wa jama’a a jihar Bauchi ba wata wahala za su sha wajen sake komawa gidan gwamnatin jihar a matsayin masu mulkan jihar ba.

Dangane da hada kai da ‘yan takarar gwamnan jam’iyyar suka yi, shugaban jam’iyyar ya bayyana hakan a matsayin babban nasarar jam’iyyar, inda ya misalta hakan a matsayin matakin kwace mulki daga APC, “Ai shine babbar murnata ma, daman idan kana da ‘ya’ya a gidanka suna neman wani abu amma kuma ba tare da hanayi ba abun murna. Wannan na nuna wa duniya mun hada kai za mu karbi mulki a jihar Bauchi da yardar Allah,” In ji Akuyam.

Hamza Kosha Akuyam ya kara da cewa, a shirye suke su ci gaba da gudanar da adalci, “Dukkanin jawabina za ku ji ina maganar adalci, wannan rashin adalcin shine muke gudu, domin rashin adalci a baya shine ya kada mu. Don haka duk wanda ya san yadda ya fito ba zai yarda ya sake komawa ba, rashin adalci ya kawo nan, yanzu mun dau darasi, duk wanda Allah bashi za mu mara mishi baya a kai ga kwace mulki a jihar,” A cewar shi.

Akuyam ya shaida cewar ba za su yi aikin kama daura ba, don haka ne ma bayyana cewar duk wanda jama’a suka zaba shine za su yarje mishi ya ci gaba da tafiyar da neman gwamnan jihar a jam’iyyar.

Dangane da wasu ‘ya’yan jam’iyyu da ake tunun zasu koma PDP kuwa, Akuyam ya shaida cewar ba za su hana kowani dan kasa zarafin shigowa jam’iyyar ba, “PDP fa uwa ce, duk wanda ya zo za mu amsheshi hanu biyu-biyu, kuma za mu bashi zarafi ya fito ya taka rawarsa ya nemi duk abun da yake so. Shigowarsu ba za su jawo mana cikas ba, domin ita PDP rumbuce,” In ji Akuyam.

Wakilinmu ya shaida mana cewar a wajen taron ne dai jiga-jigan ‘yan takarar gwamnan a karkashin PDP Sanata Bala Muhammad Kauran Bauchi da Sanata Abdul Ningi suka shaida wa dukkanin maniyarsu aniyarsu na hada kai domin mara baya wa dukkanin wanda ya samu nasarar cin zaben fidda gwamni, dukkanin ‘yan tarar sun rantse da cewar za su bi kowani daya daga cikinsu matukar aka gudanar da adalci wajen zaben fidda gwani.

A da baya magoya bayansu sun yi ta hararan juna, kwatsam sai gashi ‘yan takarar sun nuna hadin kai da kuma kaunar juna, inda kowa yayi alwashin hada kai da dan uwansa domin kwace mulkin jihar.

“Idan muka yi la’akari da yakin da ke gabanmu babu amfanin  mu tsaya muna yakar junanmu a cikin gida, yaki na nan zuwa da wadanda muke fuskanta domin kwace mulki, don haka ni a bangarena idan Allah ya baiwa dan uwana Sanata Bala Kaura nasara zan amince na mara masa baya. Babu inda za mu je muna cikin jam’iyyar PDP. Amma ina kira a yi adalci wajen fidda dan takara, domin abun da ke gabanmu ya wuce mu zauna muna yin rashin adalci wa juna, don haka ina jawo hankalin shugabanin jam’iyya a yi abun da ya dace,” In ji Sanata Abdul Ningi dan takarar gwamnan Bauchi a PDP.

Shi ma dai Sanata Bala Kauran Bauchi cewa yake, “Duk wani mabiyina da ya kushe Sanata Abdul Ningi ba da yawuna yayi ba kuma ba ruwana da shi. Abun da ke gabanmu kamar yadda yayana-kanina ya fada ya wuce mu zauna a cikin gida muna cece-kuce, don haka idan na ci na amince zan tafi da shi, idan ya ci zai tafi da ni, kai idan ma wani dan takarar ne daban ya ci za mu tafi tare, ba za mu bar PDP ba, domin ta mana komai.

“Ni bana zo na yi mulki bane, na zo ne domin na yi shugabanci na yi jagoranci saboda na ga an ci mana mutuncin a Bauchi yana cutanmu da cin zalinmu, kuma ni na amfana a PDP, don haka ina son jama’a su amfana da ni, wannan dalilin ne ya sanya na fito na ke son na gyara kurakuran da suke Bauchi,” In ji Kauran Bauchi.

Kaura ya bayyana cewar idan ya ci zai gyara matsalolin da suke jibge akwai, yana mai bayanin cewar babu abun da ya kamata kamar sun kulla zuminci a tsakaninsu, inda ya nemi jagororin PDP da kada su sanya son rai da son kai wajen zaben fidda gwani.

Tuni dai kwamitin dattawa na jam’iyyar suka fara gudanar da aikinsu a matsayin dattawa, inda jam’iyyar ta bayyana cewar ci gaba da tsare-tsare da shirye-shirye suna nan suna biyowa baya duk dai domin ganin nasararsu ta samu.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!