NNPC Na Shirin Fara Yin Ajiyar Danyen Mai Ganga Biliyan Daya Duk Shekara -Baru — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

NNPC Na Shirin Fara Yin Ajiyar Danyen Mai Ganga Biliyan Daya Duk Shekara -Baru

Published

on


Babban Manajin Daraktan Kamfanin Hukumar Kamfanin Matatar Manfetur NNPC,  Mikati Baru ya sanar da cewar Kamfanin zai kara yawan hako  danyen mai  kasar ya zuwa ganguna biliyan daya a duk shekara don a samu a cimma kudurin kashi 40 na biliyoyin gangunan danyen a shekarar 2020 mai zuwa.

Baru ya bayar da tabbacin ne a sakon sa a ranar Talata ya ci gaba da cewar kamfanin Kuma yana gudanar da aiki akan kara yawan sarrafa  gangunan danyen mai miliyan uku na a kullum.

Ya bayyana hakan ne a kasirdar da ya gabatar  a wurin taron mai taken: “inganta fanini mai da iskar Gas don ciyar da tattalin arzikin kasa a gaba”, ya kara da cewar kamfanin zai kuma tabbatar da cewar ya habaka yawan aikin sarrafa mai zuwa  500,000 na (bpd) da kuma Gas bilyan 1.5 na (scfd) nan da 2020.

Ya yabawa shirin da kuma wadanda suka shirya taron a bisa samar da zauren don tattaunawa akan fannin mai da iskar Gas a kasar nan,inda ya yi nuni da cewar taron ya zama sananne ya kuma yi fatan za a tabbatar da dorewar nasarar da aka samu.

Baru ya ci gaba da cewa tafiyar da aka yo cike take da dimbin kalubale kuma masu ban shaawa,inda ya ce mun hau tsaunuka da rafuka da kwazazabo, amma duk da haka muka jure muka kuma tsaya da kafafun mu.

A cewar sa, kamfanin yana harin  2018 da kuma fiye da hakan don kaiwa ga kasuwa wajen samar da kudi ga sabon mai da iskar Gas don aiwatar da aikin, Inda ya ce kudin da za a samar za a yi amfani da su wajen aiwatar da ayyuka kamar na sake ciyar da  (NNPC/NAOC JB Idu na aikin iskar Gas dake Kudu dana Arewa kuma sauran ayyukan sune na, NNPC/TEPNG JB’s Ikike dana NNPC/SPDC JB dake Kudu dake da alaka da  aikin iskar Gas da ake kira (Solution Step 2 Project ) da kuma sauran sababbin ayyuka.

Baru ya sanar da cewar,“muna da nufin sanya takunkumi a kan aikin biliyoyin daloli na Bonga dake Kudu dana Kudu maso Yamma na Aparo (BSWA), da zarar mun kammala kulla yarjejeniya da SNEPCO akan rikicin dake a kasa na PSC komai zai kankama.

Ya sanar da cewar akan sarrafa iskar Gas, bukatar da ake dashi a Nnijeriya abin yabawa ne idan aka yi laakari da bukatar da ake dashi a yanzu a kullum, inda ya kai yawan 4,000 kuma ana sa ran wannan jimlar zata kara hawa zuwa kimanin 7,500 nan da shekaru biyar masu zuwa.

Baru ya bayyana bewar , nan da shekaru uku masu zuwa ta hanyar abokan hadakar mu, a shirye muke wajen kara samar da isasshiyar iskar Gas da wadda ake da ita a yanzu ta 1.5bscf ya zuwa kimanin na biliyan biyar nan da shekarar 2020.

A cewar sa, gwamnati zata kuma rabar da isasshiyar iskar Gas don samar da megawatts  15 ta wutar lantarki a shekarar  2020 za mu kuma ci gaba da gudanar da aikin mu na iskar Gas guda bakwai na (7CGDP) wanda aka kafa shi don samar da kimanin aikin Gas na 3.5bscfd a kasuwar cikin gida nan da 2020.

A cewar sa, a kwanan baya “mun amince da dala biliyan  2.8 akan aikin gina bututun mai ,mai kilo mita  614 ta Ajaokuta zuwa Kaduna da Kano (AKK) don nuna cewar a shirye muke don samar da tsari akan karfafa samar da iskar Gas a lunguna da sakunan kasar nan kuma za mu ci gaba da baiwa hakan mahimmanci a kasar nan.

Ya sanar da cewar, an kuma kara farashin Iskar Gas yadda za a dinga fitar dashi waje a dinga fitar dashi waje har ila yau, garanti na (PRG)  da bankin CBN ya bayar zai taimaka wajen samarwa da gwamnati kudin shiga da kuma bunkasa fannin iskar Gas kuma akan fitar da Gas zuwa waje Baru ya ce, nufin mu shi ne mu inganta halan.

Shi ma a nashi jawabin Wemimo Oyelana, mataimakin shugaban rukunonin sarrafawa na  CWC ya jinjinawa gudunmawar da marigayi Alirio Parra, a bisa kirkiro da taron na mai da iskar Gas a kasar nan ya kuma yabawa masu ruwa da tsaki a fannin a bisa jajircewar su.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!