Connect with us

WASANNI

PSG Tana Son Siyan Coutinho Saboda Neymar Ya Zauna

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta PSG na neman sayen Dan wasan Barcelona  Philippe Coutinho, mai shekara 26, kan fam miliyan 239, domin hakan ya taimaka wurin shawo kan Neymar ya ci gaba da zama a kungiyar, kamar yadda jaridu suka ruwaito.

Wasu rahotannin kuma na cewa Neymar, mai shekara 26, na son ganin Edinson Cabani ya bar PSG. inda ake ganin akwai yiwuwar dan wasan gaban na Uruguay ya koma Napoli kamar yadda rahotanni suka bayyana daga kasar Italiya.

Manyan ‘yan wasan biyu sun samu sabani a kakar da ta gabata kan neman iko a kungiyar sai dai daga baya kungiyar ta bawa Neymar dama wadda tafi ta Cabani kuma hakan yasa dan wasan yake ganin kamar lokaci yayi da zai bar kungiyar.

Sai dai abune mai wahala kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta iya rabuwa da Coutinho wanda har yanzu baiyi shekara daya a kungiyar ba bayan yakoma kungiyar daga Liberpool a watan Janairun wannan shekarar.

Kungiyar kwallon kafa ta PSG dai tanada burin sake kashe kudi domin domin siyan manyan ‘yan wasa a kokarin kungiyar na lashe kofin zakarun turai bayan da takasa doke kungiyar Real Madrid a kakar wasan data gabata a wasan falan daya.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!