Connect with us

WASANNI

Sai Ronaldo Ya Bar Madrid Sannan Zan Koma, Cewar Hazard

Published

on

Shugaban gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Florentino Perez tuni ya warewa Eden Hazard jesi da lambar da zai saka idan har dan kwallon mai shekara 27 ya amince zai koma Bernabau da buga wasa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Real Madrid dai tana neman maye gurbin Cristiano Ronaldo wanda yake shirin barin kungiyar a wannan kakar zuwa Jubentus bayan da rahotanni suka bayyana cewa tuni Ronaldo da Jubentus suka amince da yarjejeniyar.

Tun shekaru biyu da suka gabata ne dai kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid take zawarcin Hazard sai dai dan wasan yaki amincewa da komawa kasar Sipaniyan da buga wasa saboda bayason zaman benci.

A yanzu dai Hazard yana kasar Rasha yana wakiltar kasar sa ta Belgium a gasar cin kofin duniya wanda  a yanzu haka sunje wasan dab dana karshe inda zasu fafata da kasar Faransa a yau Talata.

A kwanakin baya dai Hazard ya bayyana cewa bai san makomarsa ba a Chelsea saboda har yanzu kungiyar bata tabbatar da wanda zai zama kociyan tab a bayan da take kokarin rabuwa da Antonio Conte sannan kuma tana kokarin siyan Mauricio Serri wanda shima yabar Napoli.

Chelsea dai baza ta buga gasar cin kofin zakarun turai ba a kakar wasa mai zuwa bayan ta kammala kakar wasan data gabata a matsayi na biyar hakan yasa wasu daga cikin ‘yan wasan kungiyar ciki har Hazard din.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!