Yawaitar Hare-hare: Farashin Abinci Ya Tashi A Kakar Noman Bana — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

KASUWANCI

Yawaitar Hare-hare: Farashin Abinci Ya Tashi A Kakar Noman Bana

Published

on


Manoma dake fadin kasar nan sun bayyana jin tsoron su akan cewar tashin farashin kayan abinci a kasuwanni da ban-da-ban, zai kazanta a wananan shekarar, musamman saboda rikicin makiya da manoma da yake kara ta’azarra a wasu yankunan kasar.

Sun kuma yi nuni da cewar, gazawar gwamnatin taraya wajen shawo kan lamarin, zai iya janyo barkewar mummunar yinwa a wasu gidaje, ganin cewar sai mutane sun kashe kudi da yawa kafin sui ya sayen abincin da zau ciyar da iayalan su.

Shugaban kungiyar manoma na kasa reshen jahar Biniwe Aondoana Kuhe,wanda ya yi Magana da yawun manoman ya shedawa jaridar Punch cewar, gazawar da aka yi wajen magance hare-haren da ake yi har yanzu zai janyo yinwa a kasar.

Kuhe ya kuma koka akan cewar, yankunan da abin ya shafa inda ake yin noma, tuni makiyaya sun mamaye wurararen kuma manoman dake yankin da suka tsallake, tuni sun yi gudun hijara zuwa birane don tsirarar da rayukan su data iyalan su.

A cewar sa, Biniwe iatace akan gaba wajen noma shikafa da Doya da Waken Soya da dawa, a saboda haka in har manoma baza sui ya zuwa gonana kan su ata yaya zasu iya wadata kasa da abinci?

Ya kara da cewar, daga cikin kananan hukumomi 23 da uku dake jahar, 14 sune suke yi yin noma, inda a yanzu suke ci gaba da fuskanatr harin makiyaya.

Bugu da kari, kwamishinan ma’aikatar gona da ma’adanai na jahar  James Anbua, ya tabbatar da da maganar manoman, inda ya ce manoman jahar sunyi asarar sama da naira biliyan takwas a akan noman shinkafa kawai tun lokacin da aka fara kai hare-haren a ranar bikin zagayowar ranar sabuwar shekara.

Anbua ya ce, Biniwe tana daya daga ta biyar a kasar nan a wajen noma shinkafa kuma a wannan shekarar hakan zai yi wuya.

Ya kara da cewar, kananan hukumomin Guma da Logo suna samar da  shinkafa da waken soya tan 25,000, inda a yanzu ake asmun yan kadan a kasuwanni domin aamfanin goionar da ba a riga an girbe a ba za a iya dauko su daga gonakai ba.

A cewar sa, maharan sun kuma cinnawa gonar doya da sauran amfanin gona wuta bayan su ciyar da dabbobin su haka ya kuma janyo yadda ake yawan noman ya sauka zuwa kashi arba’in da biyar bisa dari.

Wasu daga cikin mata manoma da aka zanta dasu sun koka akan tashin farashin amfanin gona daga cikin watan Fabirairu zuwa Yuni na wannan shekarar saboda hare-haren makiyayan.

Misali sunyi ikirarain cewar a cikin watan Fabirairu, doya daya ana sayar da ita akan naira 200 a Makurdi, ya danganta da girman ta amma a watan Yuni, farashin doya daya ya karu zuwa naira 400 ko naira 500.

Wata mai sayar da shinkafa a kasuwar Wadata a Makurdi, uwargida Apeh Ogbu ta ce, farashin abincin ya tashi, inda ta ce, a watan Janairu ana sayar da mudun shinkafa akan naira 350 kuma ana irin mudun ana sayar dashi akan naira 500.

Sakataren kungiyar manoma na kasa Cif Olatunji Bandele, ya tabbatar da hakan, inda ya ce, amfanin gona da ake samarwa a Arewacin kasar nan yana da tsada a kasuwanin dake Kudancin kasar nan.

Ya ce, tattasai da albasa a yanzu sunyi tsada sosai domin kasar baki daya ta dogara ne a akan manoman dake Arewa.

Wani bincike da wakilin mu ya gudanar ya gano cewar, farashin buhun Garin kwaki a yanzu ina jin ya kai naira 7,000, kuma anfanin gona sai kara karuwa yake yi daga watan Fabirairu da kuma farkon satin watan Yuli a wasu kasuwanni dake jahar Legas.

Har ila yau, a binciken da aka gudanar a wasu kasuwannin an gano cewar a cikin watan Fabirairu, yar karamar doya daya ana sayar da ita akan naira 500, amma a yanzu ta kai naira 1,300 ko kuma naira 1,500.

Wani wake da ake kira derica ana sayar dashi akan naira 250  a watan Fabirairu, amma a yanzu ana sayar dashi akan naira 350, inda kuma Garin kwaki dake a cikin bokitin fenti da ake sayarwa akan naira 300 a baya yanzu ya kai naira 400.

Buhun shinkafa kuma ya kai tsakanin naira11,000 zuwa naira  12,000 a cikin watan Fabirairu, amma a yanzu ana sayar dashi daga naira 15,000 zuwa naira 15,500.

Har ila yau, shi ma shugaban kungiyar manoma reshen jahar Legas Cif Femi Oke, ya bayyana jin tsoron sa cewar farashin abinci zai karu saboda hare-haren makiyaya, inda ya yi kira ga gwamnatin data magance hakan.

Bugu da kari, shuigaban kungiyar manoman Rogo na kasa Also Segun Adewumi, shi ma ya koka akan hare-haren na makiyaya.

 





Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!