An Kama Masoyan Da Ke Safarar ’Yan Mata Don Su Yi Karuwanci A Legas — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

An Kama Masoyan Da Ke Safarar ’Yan Mata Don Su Yi Karuwanci A Legas

Published

on


Rundunar ‘yan sanda jihar Legas sun cafke wasu masoya, Ikechukwu Egbulefu da Bera John, da laifin safarar ‘yan mata zuwa jihar Legas don shiga sana’ar karuwanci.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Edgal Imohimi, ya bayyana cewa, wadanda ake zargin suna safarar ‘yan matan ne daga jihohin Imo da Akwa-Ibom da kuma Riber.

Imohimi ya kara da cewa, wadanda ake zargin suna yaudarar ‘yan matan ne da alkawarin zasu sama musu aiyyukan gwamnati da rayuwa ta gari a garin Legas daga baya kuma sai a ingizasu sana’ar karuwanci.

Ya ce, “A ranar 1 ga watan Yuli na shekarar 2018, daidai karfe 2, rundunar ‘yansandan mu suka samu rahoton cewa, Ikechukwu Egbulefu da Bera John suna safarar ‘yan mata zuwa cikin jihar.

“Muna samun rahoton ne muka aika jami’anmu na ‘Federal Special Anti Roberry Skuad’ inda suka gudanar da bincike, daga nan ne aka cafke Ikechukwu Egbefule dan shekara 27 daBera John ‘yar shekara 26 a otal din Wagbas dake unguwan Ajah, a Legas.

“Wadanda aka yi safarar nasu kuma aka samu cetosu sun hada da Helen Dickson, ‘yar shekarar 22 da Deborah Dabid ‘yar shekara 18 da kuma Chiwendu Onyekachi ‘yar shekara 18.

Kwamishinan ‘yan sandan ya kara da cewa, ya ce, wadanda ake safarar sun ce said a wadanda suka yi safarar nasu suka kaisu wajen wani tsafi a Epe-Ijebu a nan jihar inda su kayi rantsuwar ba zasu gudu daga otal din ba kuma duk kudaden da suka samu daga zinace zinacen da suka yi da mazaje zasu kai kudin ne ga Bera John.

Daya daga cikin wadanda aka yi safarar, Onyekachi, ta ce, “Na san Egbulefu tun daga kauyenmu a jihar Imo. Ya sanar da ni cewa, ya sama mani aiki ne na mai saye da sayarwa a wani otal a legas, saboda haka na bi shi inda ya gabatar dani ga John, wanda ya gaya mani iri nau’in aikin d azan rika yi a otal din, da ban amince da aikin ba, sai suka yi mani barazana korani waje da kuma wahalar dani.

“Mun yi rantsuwar ba zamu gudu ba. sun tafi damu wajen wani boka inda ya yi anfani da gashin kanmu dana al’auranmu ya hada magani, suka umurcemu muyi wanka da magani, sun kuma bamu wani bakin abu muka ci. Sun ce in harm un gudu zamu haukace.

“Sun mayar dani karuwa, na kan yi jima’i da maza fiye da 10, a rana na kan hada fiye da naira 20,000, har lokacin da nike al’ada nakan yi jima’i da maza.”

Wata da aka yi safararta, Dabid, ta ce, “Sun yi nami bayanin cewa, matar Egbulefu na bukatar wanda zai yi mata ‘yar daki a Legas. Sai da na iso Legas na fahinci karuwanci aka kawo ni. Da yake ban san kowa ba a nan sai nayi shawarar in ci gaba da karuwanci da nifin in dan tara kudaden d azan koma gida, a halin yanzu mako na 2 kenan da fara karuwancin.

“A rana kamar Litinin ko Laraba na kan hada Naira 10,000 zuwa Naira 15,000 daga jima’i da mazaje 4 zuwa 6. Amma a karshen mako inda na kan kwanta da maza kamar 8 zuwa 10 nakan hada Naira 20,000.”

Wadanda ake zargin sun amince da laifinsu na amfani da ‘ya matan a harkar karuwanci. Ogbulefu ya ce,, “Na sanar dasu cewa, aikin karuwanci zasu fada in mun iso Legas sun kuma amince. Mun amince tsakaninmu na cewa, in sun yi karuwancin na shekara 1 zamu basu naira miliyan 1.

“Saboda ban yarda da kowa ba, kuma bana son ya zama an samu matsala wajen basu kudadensu da kuma maganar cika alkawari, sai na bukaci su yi rantsuwa sabpda kada mu ci amanarsu suma kada su ci amanarmu, shirn dana yi shi ne in sallamesu a karshen shekara.”

John, wadda ta fito daga jihar Abia, ta bayyana cewa, ita take karbar kudaden da aka samu na karuwanci daga hannun wadanda suka yi safarar.

Ta kuma kara da cewa, “Na kan karbi Naira 6,000 wani lokaci kuma nakan karbi Naira 10,000 daga ‘yan matan yayin da suka tashi aiki. Onyekachi ce tayi korafin jama’a basa amfani da ita yadda ya kamata, a kan haka ta nemi ko a kwai inda za a kaita don a yi maganin da za ta rinka samun mutane yadda ya kamata, saboda haka ne na kaita wajen boka, inda ya bukaci a kawo kaza da sabulu ya bukaci suyi wanka dasu domin wanke bakin jinni dake tattare dasu.”

Kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana cewa, za a gurfanar da wadanda ake zargin gaba kotu nan bada dadewa ba.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!