Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Dalibi Ya Dirka Gadar Legas Saboda Tsoron ’Yan Sanda

Published

on

Wani dalibi dake zagon karatu na biyu kuma mai koyon darasin kimiyya da kira a jami’ar jahar Kwara mai suna Oluwadara Adedayo, a yanzu haka yana cikin jin jiki a bisa zargin tsallen da ya yi ya fada a cikin gadar  Cele-Okota dake jahar Legas.

Adedayo ana zargin ya yi hakan ne bayan da yan sanda dake sashin masu yaki da masu sace mutane da jahar suka biyo shi a sukwane.

Majiyar mu ta bayyana cewar, Adedayo, wanda a yanzu haka yake kan koyon sanin makamar aiki a jahar, yana kan hanayar sa ce ta zuwa yankin Yaba a ranar litinin lokacin da lamarin ya auku a daidai madakatar mota ta Cele.

An ruwaito cewar, bayan da yan sandan suka dakatar da dalibin dan shekara ashirin da hudu, sun yanke shawarar chaje wayar sa ta tafi da gidan ka, inda suka ga na’urar sadarwa da internet a jikin sa.

A cewar sa, yan sandan sun kuma umarce ya shiga motar su amma yaki ganin cewar basu gaya masa mene laifin sa ba.

Adedayo, wanda yace babu wani abin laifi da suka same shi dashi yan sandan sun kuma cacume shi suka jefa shi a cikin motar su.

Ya kara da cewar, danaga na samu damar arcewa sai na dira saboda darasin dana taba shiga a hannun yan sanda.

Ya sanar da cewar, a yan kwanukan baya yan sanda sun cafke ni suka zarge ni da cewar ni mai damfara a kafar internet ba tare da wata hujja ba.

A cewar sa, sun dauke ni suka kai ni yankin FESTAC suka kwace mini naira 2,000  kafin su sake ni sai da naji jiki kafin inje gida a ranar.

Yace, daya daga cikin yan sandan ya biyo ni a guje akan babur bayan dana tsaya sai ya yi sauri ya jingine babur din ya auna ni da bindiga ya yi min barazanar in na dira kan gadar zai harbe ni.

Adedayo yace, sai da ya fita daga cikin hayyacin bayan da ya dira a cikin gadar, inda takwarorin suka zo wurin kuma wasu masu jin kai ne suka kai ni asibiti daga baya kuma aka garzaya dani zuwa babban asibiti na Isolo daga nan kuma aka mayar dani asibitin kashi na kasa dake Igbobi.

A cewar sa, ban kai rahoto ga ofishin yan sanda ba domin ba’a jima da sallamo ni daga asibiti ba.

An kira layin wayar kakakin rindinar yan sandan jhar CSP Chike Oti don jin ta bakin shi amma wayar a kashe kuma an tura masa sakon karta kwana amma har zuwa lokacin hada wannan rahoton babu amsa daga gare shi.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: