Connect with us

WASANNI

Dan Wasan Arsenal Wilshere Ya Koma Westham

Published

on

Tsohon dan wasan Arsenal Jack Wilshere ya koma kungiyar kwallon kafa ta West Ham kan yarjejeniyar shekara uku, inda ya ce ya koma kungiyar da ya dade yana kauna tun yana yaro.

Kwantiragin dan kwallon mai shekara 26 ya kare da Arsenal a karshen watan Yuni kuma sabon mai koyar da kungiyar ya bayyana cewa ba zai dinga amfani dashi ba yadda yakamata wanda hakan yasa Wilshere yake ganin ba zai iya zaman benci ba.

“Har yanzu ina tuna lokacin da nake goyon bayan West Ham a lokacin da ina karami, na sha kallonsu a filin wasa na Upton Park,” a cewar Wilshere.

West Ham na kuma dab da kulla yarjejeniya domin siyan dan kwallon Ukraine Andriy Yarmolenko daga kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund ta kasar Jamus.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!