Guguwar ’Yan A Kwafe – A Watsa A Yanar Gizo ‘Copy and Paste’ — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Guguwar ’Yan A Kwafe – A Watsa A Yanar Gizo ‘Copy and Paste’

Published

on


A wannan makon ina so ne na yi tsokaci dangane da wata guguwa wacce ta taso, ta ke neman zama annoba, amma ta fi kama da shisshigi da kokarin neman suna. Ganin yadda lamarin yayi kamari ne ya sa na ke son mayar da hankali a kai don yin nazarin inda gizo ke sakar.

Idan har zai yiwu a mayar da wani lamari ya zama yaayi, ko kuma a rika yin rige – rige wurin aikata wani aiki, lallai za a samar ko kuma a jefa al’umma cikin wani irin yanayin da bai kamata ta tsinci kanta a ciki ba. A maimakon a sa rai da nagarta a tsakanin al’umma, ta hanyar fadada tunani, da yawaitan nazarce nazarce, bincike na musamman, karance – karance, da sauransu, sai dai ma a samar da akasin haka.

Guguwar yanar gizo ba za a kira ta da wani sauyi abin ki ko kyama ba, bilhasali ma ta zo da alherai masu yawan gaske. Yanar gizo ta zamanto wata kafa ta isar da sakonni cikin gaggawa, kuma kafa wacce a ke neman litattafai da ilimi. Masu nazarori a kan mabambanta lamurra ma sukan samu saukin nazarinsu sosai da taimakon yanar gizo. Da zuwan yanar gizo ne a ka rage aiki da ‘Online Kuestionnarie’ wurin tattaro ra’ayoyin jama’a dangane da wani lamari.

Harkar yanar gizo wata aba ce wacce za a iya kiranta da bakuwa, yanar gizo ta ‘Internet’ ta samo asali ne daga ‘Arpnet’ wanda a ka assasa a cikin shekarar 1969, amma ita Kalmar ta ‘Arpnet’ an samar da ita ne a shekarar 1974. Shi kuma bangaren ‘World Wide Web’ wanda a ka fi sani da WWW an kirkire shi ne a tsakankanin tis’inoni 1990s, a lokacin da a ka samu ci gaba wurin samuwan su I-mel. Haka kuma bangaren da a ke laluben yanar gizo da shi, wato ‘Internet Edplorer’ an fara aiki da shi ne a shekarar 1995.

An samar da sashen binciken yanar gizo na ‘Google’ a shekarar 1998. Sashen adana bayanai na ‘Wikipedia’ kuma ya fara aiki a shekarar 2001. Kafar sadarwa ta ‘Facebook’ da ‘Myspace’ da ‘Youtube’ duk sun fara aiki ne a tsakiyan 2000s.

Kafar sadarwa ta ‘Whatsapp’ an kirkire ta ne a shekarar 2009, wanda ta samu bisa hadin gwiwar wasu matasa biyu, wato Brian Acton da Jan Koum, wanda kuma dukkaninsu ma’aikatan kamfanin ‘Yahoo’ ne. mutanen biyu sun bar aiki da kamfanin ‘Yahoo’ ne a shekarar 2007, bayan wani lokaci suka nemi aiki da kamfanin sadarwa na ‘Facebook’ amma a ka yi watsi da bukatarsu. Daga nan ne suka samarwa da kawunansu mafita ta hanyar assasa kafar sadarwa ta ‘Whatsapp’.

Na dan yin fashin baki a kan wadannan kafafen sadarwa na yanar gizo ne saboda ko ba komi su ne wadanda a ka fi watangaririya a cikinsu a ‘yan shekarun nan. Yanayin yadda wasunmu ma ke ziyartarsu da nuna musu damuwa da shauki, ko karatunsu ko kasuwancinsu ko iyalansu ba su samun wannan tagomashi.

Daga cikin tsiyatakun da yanar gizo ta kawo sun hada da bibiyan shafukan batsa da mutane ke yi, har ta kai ma mutum ba sai ya nemi zuwa yawon gani da ido a shafukan batsan ba, da kansu su ke cillo ma mutum talla, wai don ya samu shi ma ya leka.

Wani abokina da ya je kasar Amurka, bayan ya dawo, ya zo mu na hira sai ya ke ce min ai mutanenmu munafukai ne, ga yawan fadin tsoron Allah da riko da addini, amma kuma sai yawaitar abin kunya. Na ce, lafiya kuwa? Sai ya ce min ai a zuwanshi Amurka, sun ziyarci kamfanin ‘Google’ inda a chan ne a ka tambaye su wanne daga kasashen da su ke. Sai kowa ya fadi sunan kasarsu sai a duba a ga ‘yan kasar me suka fi dubawa a ‘Google’.

Abin kunya da takaici, ko da aka zo kanshi, a ka duba me ‘yan Nijeriya suka fi dubawa a ‘Google’ kawai sai ga kaso mai yawan gaske ya nuna cewa ‘yan kasarmu sun fi bibiyan shafukan batsa ‘Pornography’. Alhali sauran kasashen Afrika da a ka duba, irinsu Sudan, Kamaru, da sauransu sai ga shi a na ganin wasu sun fi duba yadda a ke kere – kere, wasu kuma sun fi duba yadda a ke binciken kimiyya.

Wannan labarin da abokina ya bani, ya bani haushi sosai da takaici, ba don ina da fahimtar ‘Sauyi a cikin al’umma’ ba, wanda na samo sakamakon ilimin kimiyyar zamantakewa, da na yi Allah wadai da samuwar yanar gizo ga ‘yan Nijeriya. Amma ban ce hakan ba, ba kuma zan ce ba. Ko ba komi na san a kowanne sauyi da kan zo ga al’umma, akwai bangaren da ke da sha’awa da kuma bangaren Allah wadai da tir.

Zuwan wayoyin Chana, wadanda da ‘yar Nairarka dubu 3 ko dubu 2,500 za ka samu mai kamo talabijin da Rediyo. Tsaf za ka nemi alfarmar wani ya turo maka na’urar ‘Shareit’ ko ‘Dender’, sai a turo maka kafafen sadarwa, irin su ‘Whatsapp, Facebook’ da sauransu. Abin ya sauko, da naira 60 sai ka ga mutum ya siyi ‘data’ wacce za ta rika shigar da shi kafafen sadarwan.

Irin wadannan mutanen, wadanda hatta ma yadda a ke amfani da wayar salula mai sarrafa yanar gizo ba su iya ba, su na nan fululu sun cika yanar gizo a Nijeriya. Su na nan, ban da addabar jama’a babu abin da su ke yi. Su batawa kawunansu lokaci, su bata na wasu.

Abin takaici, idan har irin wadancan mutane za su kasance cikin guguwar a kwafe – a watsa, to shi kuma mutumin da ke ganin shi mai ilimin zamani ne da wayewa fa? Wanda akalla ya san duniya, kuma yayi wayewan da ya kamata a ce ya na ita tantancewa tsakanin fari da baki. Amma inaaa, wani idan yayi kwanton bauna ya kwafo wani rubutun, da ya watso shi za ka ji kaman zuciyarka ta buga don takaici.

A wannan guguwar wai har da masu kiran kansu ‘yan jarida, sai ka ga mutum ba kunya ba tsoron Allah, ya kwafe rubutun wani ya cire sunan mai rubutun, ya sa nashi, sannan ya fara watsawa. Wasu kwararru a wannan harkar ta a kwafe a watsa, idan ma da za su rika yin hakuri su na karanta abin da za su watsa din da an samu sauki.

Shin wai ma, kafin ka kwafe ka watsa, ka kan yi la’akari da me ke kumshe a cikin sakon, shin ya dace da addininka, ya dace da al’adarka, ya dace da maslahar rayuwarka? Shin zai iya kawo sabani ko rikici cikin al’umma? Ko zai iya zama sanadin salwantar rayuka? Me zai hana ka yi tunani, ya kai kwararre a harkar a kwafe – a watsa?

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!