Har Yanzu Real Madrid Tana Zuciya Ta -Hazard — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Har Yanzu Real Madrid Tana Zuciya Ta -Hazard

Published

on


Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Edin Hazard, dan kasar Belgium, ya bayyana cewa har yanzu kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tana zuciyar sa duk da cewa tsohon kociyan kungiyar, Zidane, yabar aikin kungiyar.

Zidane dai ya bayyana aniyarsa a fili ta daukar Hazard zuwa Madrid sai dai tashinsa ya zama yasa aka fara tunanin abune mai wahala dan wasan ya koma kungiyar sakamakon tashin na Zidane.

Hazard ya ce har yanzu kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid bata rasa komai ba duk da cewa Zidane yabar kungiyar sannan kuma ya ce yana fatan ganinsa a kungiyar wani lokaci anan gaba.

“Ina cikin farin ciki a kungiya ta ta Chelsea kuma har yanzu babu kungiyar data kawo min tayin komawa kungiyar” in ji Hazard

Hazard ya kara da cewa “ Tabbas Zidane kwararren mai koyarwa ne sannan kuma Real Madrid tana sharewa kowa hawayensa haka zalika har yanzu saka rigar Real Madrid abune mai dadi amma ina cikin farin ciki a Chelsea”

Real Madrid dai har yanzu tana burin ganin ta siyo Neymar, daga kungiyar kwallon kafa ta PSG sai dai idan bata samu damar siyan dan wasan ba zata nemi Hazard idan Ronaldo ya koma Jubentus.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!