Connect with us

MANYAN LABARAI

Kashe-kashe: ’Yan Siyasa Ke Shirya Min Makarkashiya –Buhari

Published

on

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kara nanata cewa ‘yan siyasa ne ke shirya mishi makarkashiya kan kashe-kashen da ake aiwatarwa a Nijeriya wanda ake fakewa da sunan rikicin makiyaya da manoma.

idan dai ba a manta ba, dimbin jama’a ne suka rasa rayukansu sakamakon wannan rikici na makiyaya da manoma wanda ya ki ci, ya ki cinye wa. Wanda a kodayaushe a ke daura alhakin kashe-kashen akan makiyaya.

Shugaba Buhari ya bayyana batun kulla masa makarkashiya ne jiya a wurin babban gangamin jam’iyyar APC wanda ya gudana a garin Ado Ekiti, Babban birnin Jihar Ekiti lokacin da suke gangamin nuna goyon baya ga dan takarar gwamnan Jihar a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Dakta Kayode Fayemi.

Buhari ya ce, da gangan ‘yan siyasar suke kara rura wutar rikicin, inda suke zarginsa da cewa ya ki daukar matakin da ya dace ne saboda kasantuwarsa Bafulatani.

Shugaban ya ce, wannan zargi ne marar tushe da madafa, domin gwamnatinsa a tsaye take kan lamarin, domin tabbatar da bayar da kariya ga rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijeriya.

Ya ce; “Bari na yi karin haske kan rikicin makiyaya da manoma da ke faruwa. Da yawan ‘yan siyasa suna ci gaba da shirya min makarkashiya kan wannan lamari, inda suke cewa wai na ki daukar mataki ne don nima Fulani ne.

“Wannan sharri ne da kage kamar yadda na sha fadi a baya, babu abin da na sa a gaba baya ga kare rai da dukiyar al’umma.” inji shi.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!