Kungiyar Musulmi Ta Yaba Wa Makarantar Shari’a Don Kiran Firdausi Amasa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Kungiyar Musulmi Ta Yaba Wa Makarantar Shari’a Don Kiran Firdausi Amasa

Published

on


Farfesa Ishaq Akintola ya yaba wa Makarantar Shari’a don kiran Firdaus Amasa tare da barinta ta sanya hijabi. Akintola, wanda shi ne Daraktan, kungiyar Kare Hankin Musulmai (MURIC) ya sanar da hakan a wata sanarwa a ranar Laraba a Jihar Legas.
Makarantar shari’a ta Najeriya ta kira Amasa da Musulmai 11 zuwa bar a ranar Talata; An ba su izini su saka hijabi yayin da suka shiga wasu daliban 1,550.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an hana Amasa shiga cikin zauren don bikin a watan Disamba na shekara ta 2017. Kungiyar MURIC ta yi kira ga hukumomi su ba wa sauran daliban musulmi mata wadanda suka yanke shawarar sanya hijabi damar sawa a kiran da za a yi a nan gaba don halartar bikin.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!