Ma’aikatan FRCN Kaduna Sun Ba Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 21 — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Ma’aikatan FRCN Kaduna Sun Ba Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 21

Published

on


Ma’aikatan Gidan Radiyon Tarayya FRCN dake Jahar Kaduna a karkashin kungiyar ma’aikatan Radiyo da Talabijin ( RATTAWU), sun gudanar da zanga-zangar lumana akan matsalolin da gidan Radiyon ya jima yana fuskanata.

A hirar ta manema labarai jim kadan da kammala zanga-zangar da kungiyar ta jagoranta jiya Litinin a harabar gidan Radiyon, Shugabar Kungiyar ta RATTAWU Kwamarade Halimatu S. Abdulmumini ta ce,” makasudin da ya sanya muka gudanar da wannnan karamar zanga-zanga ita ce, gidan Radiyo  na tarayya dake fadin kasar nan na FRCN baki dayan su, suma sun tsuduma a cikin irin wanana zanga-zangar don nuna koken su akan yadda gidajen Radiyon suka fita daga cikin hayyacin su na rashin kayan aiki da suka shafe kusan shekaru talatin zuwa sittin da suka shige da ma’aikatan gidan suke amfani dasu.

Da aka tambaye ta ko suna shirin kulle gidan Radiyon ta bayyana cewar,” a’a baza mu rufe ba amma matakin mu na gaba shine zamu basu takardu na wa’adin kwanaki ashirin da daya, inda in har ba’a dauki wani mataki ba zamu san abinda zamu yi a gaba.”

Ta koka da cewar, tun lokacin marigayi Firimiyan Arewa Ahmadu Bello Sardauna ake amfani da kayan kuma duk sauran maleji ne ake yi kawai, muna so ne a chanza a dawo dasu na zamani.”

Da aka tambaye ta kafin gudanar da zanga-zargar ko sun taba gabatar wa da gwamnatin tarayyar da koke, Kwamarede Halimatu ta ce,” tun kafin yau mun munyi-munyi amma shiriu shi ya sa muka dauki matakin gudanar da wannan zanga-zangar don mu nuna bacin ran mu a fili.”

Ta yi nuni da cewar,ba wai muna yin fito na fito da mahukuntan gidan Radiyon ko gwamnatin tarayya bane, muna kawai son mu janyo hankalin gwamnatin tarayya a karkashin mulkin mai girma shugaban kasa Muhamamdu Buhari da ya dubi gidajen Rediyon FRCN

dake daukacin fadin kasar nan, musamamn gidan Radiyo Kaduna  da rahama don samar da kayan aiki na zamani don ma’aikatan su samu sukunin gudanar da ayyukan su daidai da zamani.

A cewar Halimatu, gidan Radiyo na Kaduna baya amfana da komai daga gwamnatin tarayya kuma dukkan kayan aikin gidan sun durkushe haka walwalar ma’aikatan bata wani taka kara ta karya ba haka muna fama da rashin Kujerun da teburan aiki, kuma dukkan wannan laifin mun dora su ne kachokam akan gwamantin tarayya ba akan mahukantan gidan Radiyon ba.

Ta bayyana cewar ma’aikatan gidan Radiyon suna jin jiki, musamamn masu tarawa gidan kudin shiga domin duk iya kokarin da suke yi wajen samowa gidan tallace-tallace, hakan yana faskara domin janaretocin da na’urorin mu yada bayanai basa yin aiki kamar yadda ya kamata.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!