Na Amsa Kiran Yin Takarar Shugabancin Kasuwar Dawanau Ne Don Ci Gaban Kasuwar -Mahadi Abdullahi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Na Amsa Kiran Yin Takarar Shugabancin Kasuwar Dawanau Ne Don Ci Gaban Kasuwar -Mahadi Abdullahi

Published

on


Na amsa kiraye-kirayen neman yin takarar shugabancin kasuwar Dawanau ne dan kyautata ci gaba da bunkasar kasuwar daidai da tafiyar zamani. Daya daga cikin yan takarar shugabancin kasuwar saida kayan abinci na Duniya da akafi sani da kasuwar Dawanau. Alhaji Mahadi Abdullahi Muhammad ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai a Kano.

Ya ce an yi ta kiraye-kiraye akan ya fito ya tsaya wannan takara musamman dan ana gann akwai gudummuwa dazai iya bayarwa na kawo ci gaba da bunkasa kasuwar dan haka ba yanda za’ayi dole ya amsa wannan bukata ta yan’kasuwar ta Dawanau ya fito takara.

Alhaji Mahadi Abdullahi ya ce akwai matsaloli na zahiri dana badini da suke damun Kasuwar ta Dawanau da idan yakai ga nasara  za su hadu da yan’kasuwar su dinkesu sannan akwai wanda za su jawo Gwamnati  tun daga ta tarayya har ta jaha da karamar hukuma dan a samarda ci gaban kasuwar wacce  tana mu’amala da mutane daga sassan kasashen Duniya daban-daban.

Yayi nuni da cewa ana kawo arziki daga kasashen Duniya jaharnan ta kasuwar dan haka yanada mutukar muhimmanci a jawo hankalin Gwamnatoci su shigo su kara karfafawa yan kasuwar ta zamanantar da ita don ta rika tafiya daidai da muradin zamani na kasuwanci wanda hakan zai bunkasa tattalin arzikin jahar Kano da kasa da kasa baki daya.

Alhaji Mahadi ya ce zai hada kai da Gwamnati dan kewayeta da katanga  a samarda hanyoyi a cikin kasuwar da kuma fitilun tituna da a zamanantar da ita dan kara inganta harkokin tsaro da ci gaba da inganta dangantaka da take wakana tsakanin ’yan kasuwar da bangarorin jami’an tsaro da ke bayar da kulawa ga kasuwar.

Ya yi nuni da cewa akwai kalubale da suke fuskanta na sayen kayan abinci a wajen mutane da suke kawowa daga sassa daban-daban bayan sun saya sun biya sai daga baya a biyo a ce musu wannan kaya na rashin gaskiyane su kuma basa iya gane gaskiyar wadanda suka kawo musu kayan abode suna zuwane cikin kamala hakan yana jawowa wasu yan kasuwar dinbin asara dan haka za su hada kai da jami’an tsaro dan ganin an maganta aukuwar irin wannan matsalar da kuma kare dukiyoyi da rayukan yan’kasuwar.

Dan takarar neman shugaban kasuwar na Dawanau yayi kira ga dukkan yan takara da suka fito da cewa dukkansu manufarsu daya ce ta neman kawo ci gaba ga bunkasar kasuwar kuma ya san ba wanda ya fito dan ko  a mutu ko a yi rai ba,  duk wanda Allah ya bai wa nasara ya kamata a bashi goyon baya daya kamata dan ci gaban kasuwar.

Alhaji Mahadi ya kumayi kira ga kwamitin zabe na kasuwar akan a tsaya wajen gudanar da zabe na adalci duk wanda yakai ga nasara a tabbatar dashi sannan su kuma yan kasuwa masu zabe su tsaya su zabi cancanta wanda sukeda yakinin zai kai kasuwar ga samun gagarumar nasara na ci gaba da bunkasar harkokin kasuwancinsu.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!