Connect with us

LABARAI

NUJ Ta Bukaci A Samar Da Mafita Kan Yawaitar Aiyukan Ta’addanci A Nijeriya

Published

on

Kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Bauchi ta kirayi gwamnatin tarayyar Nijeriya ta fitar da mafita na karshen wanda zai kai ga kawo karshen yawaitar tashin-tashi da ake yawan samu a fadin kasar nan ta Nijeriya.

Kungiyar ta yi kiran ne a jiya cikin rahoton bayan babban taronta na zango-zango domin bayyana aikace-aikacen da kungiyar ta gudanar a cikin zango, taron ya gudana ne a cikin sakatariya da ke Bauchi.

Isa Hassan Jarawa na BATB da Bulak Afsa ta NTA sune suka yi aikin fitar da sakamakon, inda Hashimu Umar Bulkachuwa ya dafa musu, sakamakon bayan taron ya kuma nuna godiyar kungiyar ga gwamnatin jihar Bauchi a bisa amincewa sake sabunta sakatariyar ‘yan jarida da ke Bauchi wanda gwamnatin ta amince za ta yi.

NUJ dai ta tattauna muhimman batutuwa da suka jibinci ci gaban aiki jarida, ci gaban kasa da kuma tattauna matsalolin da ‘yan jarida ke fuskanta a halin yanzu, taron ya kuma yi bayani dangane da bukatar da ke akwai ga ‘yan jarida da su sanya kwarewa da kuma yin taka-tsantsan wajen kawo rahotonnin zabe ganin cewar an kusa fara gangamin neman zabe, an jawo hankalin ‘yan jarida da kada suke kauce wa ka’idar aikinsu da kuma biye wa son rai, baya ga nan an tattauna muhimmancin yin rahotonnin da za su kawo ci gaba ba tayar da tarzoma ba.

NUJ ta ce, “Taron ya gode wa gwamnatin jihar Bauchi a bisa kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da ‘yan jaridan jihar; a bisa haka ma a kwana-kwanan nan an samu ci gaba da wanda gwamnatin ta amince za ta sake sabunta cibiyar ‘yan jarida da ke Bauchi,” In ji rahoton bayan taron.

Har-ila-yau, NUJ ta roki gwamnatin tarayya ta sanya hankali wajen gyara hanyoyin da suke jihohin kasar nan domin kare rayukan ‘yan kasa da lafiyarsu, kungiyar ta yi la’akari da yadda hanyoyi suka lalace don haka ne ta jawo hankalin gwamnatin tarayya kan hakan.

Haka kuma, ‘yan jaridan sun amince da kira ga masu hanu da kumbar susa da su bayar da tasu gudunmamwar wajen gina jami’o’i masu zaman kansu a jihar Bauchi domin kyautata sha’anin koyo da koyarwa, baya ga nan, NUJ ta jinjina wa kokarin wanda ya assasa gidan rediyo mai zaman kanta a jihar Bauchi mai suna ALBARKA, inda aka bayyana hakan a matsayin hanyar samar wa mambobinta aiyukan yi.

Taron ‘yan jaridan ya kuma bukaci dukkanin gwamnatoci a dukkanin matakai da su maida hankulansu wajen samar wa al’umman karkara ababen more rayuwa musamman ta fuskancin kyautata yanayin haihuwan jarirai ta fuskacin kyautata sha’anin ruwan amfanin yau da gobe wa al’umman karkara.

NUJ ta nuna damuwarta kan yadda wasu ma’aikatu masu zaman kansu basu iya biyan ma’aikatansu albashi, don haka ne NUJ ta roki masu mallakin ma’aikatu da suke tabbatar da walwala da jin dadin ma’aikatansu a kowani lokaci ta hanyar biyansu albashi da kuma yi musu kyautuka domin kara musu azama a bakin aiki.

Taron zango-zango na NUJ ya kuma jawo hankalin dukkanin wani dan jarida a fadin kasar nan da ya tabbatar da ya yi sabon rijista da uwar kungiyar ‘yan jaridan take kan yi a halin yanzu, NUJ ta bayyana cewar ta hanyar yin rijistan ne kawai mutum zai samu zarafin sahalewarsa a matsayin mamba ko akasin hakan.

Shugaban ‘yan jarida na jihar Bauchi Kwamared Ibrahim Malam Gobe shine ya jagoranci zaman, inda bangarori da ofisoshin da suke karkashin cibiyar suka gabatar da rahotoninsu, Malam Goje ya sha alwashin ci gaba da yin duk mai iyuwa wajen kyautata aikin jarida a jihar Bauchi.

Mukaddashin shugaban ‘yan jarida na kasa, mai girma Jarman Alkaleri Kwamared Mukhtar Gidado shine ya sanya ido kan yadda tattaunar ta gudana, ya kuma albarkacin taron da shawarori masu fa’idantarwa.

Mambobin da suke karkashin kungiyar ta NUJ daga kowace fanni a fadin jihar ne suka gudanar da wannan taron, inda suka tattauna muhimman batutuwa hade da gabatar da rahotonin aikace-aikacen da suka gudana a cikin zango da mambobin kungiyar, ababen da suka wakana sun hada da bayyana adadin kudaden da suka shigo wa kungiyar da yadda aka yi suka shigo, hadi da bayyana yadda aka yi aka kashe su.

Kungiyar dai ta yi jinjina wa mambobinta da suka rigamu gidan gaskiya hade da yin shiru na mintuna domin karramasu.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!