Connect with us

LABARAI

Wani Mutum Ya Kashe Uwar Matarsa A Kebbi

Published

on

A  jiya ne rahotani ke fitowa daga garin Bangu a cikin gundumar Mahuta ta karamar hukumar Fakai da ke jihar kebbi cewa wani mutum ya kashe uwar matarsa kan sakin matar tasa da yayi wata daya da ya gabata .

Majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ta shaidawa LEADERSHIP A Yau cewa; “Alhaji Manu Tambaya dan shekaru 40 da haihuwa ya saki matarsa ne bayan wani sabani da suka samu a tsakaninsu wata daya da ya gabata, inda kuma a jiya ya je garin Bangu gidan su matar domin shirin mayar da aurensa da ita.Bayan an kai karshen maganar mayar da auren ne, sai uwar matar tasa da ba a bayyana sunanta ba, ta bukaci da ya koma, za su mayar masa da matar idan dare yayi. Inda shi kuma ya ce bai yarda ba, daga nan kawai ya zare adda, ya far wa uwar matar da sara hart a mutu”.

Haka kuma majiyar ta ci gaba da cewa “ bayan ya kashe uwar matarsa ya kuma ci gaba da saran wasu mutane biyu daga cikin gidan na su matar tasa”. Daga nan kuma sai ya gudu, amma kuma bai tsira ba kan gudun da yayi, inda mutanen garin na Bangu suka yi tara-tara suka kamashi suka tika masa kishi har sai shima ya mutu har lafira.

Jaridar LEADERSHIP A Yau ta nemi jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar ta kebbi kan  aukuwar lamarin da wani bafulatani dan shekaru 42 Mai suna Alhaji Manu Tambaya da ake zargi da kasha uwar matarsa kan sakin aure a tsakaninsa da matarsa da ba’a bayyana sunan ta ba , Mai Magana da yawun rudunar  watau PPRO DSP Mustapha Suleiman ya tabbatar da aukuwar lamarin a garin na Bangu a Mahuta na cikin karamar hukumar mulki ta Fakai da ke a jahar kebbi.

Ya kuma ci gaba da cewa matsalar aure ce tasa dan shekara 42 ya kashe uwar matar tasa, saboda tace masa ya bari har da dare a maida matar tasa , sai ya nuna bai yadda ba , daga nan ne ya fitar da adda daga cikin jikinsa inda yayi amfami da ita ya kashe uwar matar tasa Aisha Barto ‘yar shekaru 40 har lafira.

Bugu da kari yace “ suma mutanen garin sun samu nasarar kamashi bayan ya gudu , sai suka buge shi ya mutu har lafira”, bayyanan da muka samu ga mutanen da ke kusa da inda abin ya faru. Domin kafin jam’ar rundunar ta ‘yan sanda ta samu labarin faruwar lamarin sun kashe junnansu.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!