‘Yan Siyasa Ne Suka Dauki Nauyin Shirya Zanga-Zangar Bata Wa Dogara Suna -NEYPF — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

‘Yan Siyasa Ne Suka Dauki Nauyin Shirya Zanga-Zangar Bata Wa Dogara Suna -NEYPF

Published

on


A ranar Litinin da ta gabata ne wasu gungun matasa maza da mata suka yi tattali a kan titinan a jihar Bauchi suna masu bayyana Kakakin Majalisar Tarayya, Barista Yakubu Dogara a matsayin mutumin da bai son jihar Bauchi da al’umman jihar, suna masu nuna sa a matsayin wani shugaba marar nagarta.

Masu zanga-zangar duk da babu bayyana kansu a matsayin kungiya kaza ba, sun dai fara gangamin ne daga titin Wunti suka nufi wasu titunan jihar jihar gami da kitse hancin zanga-zangar tasu a gidan gwamnan jihar Bauchi.

Daga cikin ababen da masu zanga-zangar suka bayyana, sun hada da cewar Dogara bai son jama’an jihar Bauchi da ci gaban jihar Bauchi a sakamakon kin zuwa ya yi wa jama’an jihar jajen ibtila’in Guguwa da Gobara wanda ya sami jihar a kwanakin baya, sai aka ganshi ya je jihar Filato domin jajanta wa jama’an jihar kan rikicin da ya barke a jihar, wannan lamarin ya fusata wasu jama’an jihar Bauchi.

Masu zanga-zangar sun kuma yi zargin cewar Dogara bai son shugaban Nijeriya Buhari, suna masu bayyana cewar yana shirin tatile kafar Buhari, gami da sauran ababen da suka bayyana kan Kakakin Majalisar.

Tuni dai kungiyar ci gabantar da matasan shiyyar Arewa Maso Gabas wato ‘North East Youth Progressibe Forum’ ta fito fili gami da sukar zanga-zangar da aka yi wa Kakakin Majalisar.

Kungiyar ta bayyana hakan a matsayin wani shiryenyen shiri da wasu ‘yan siyasa suka kitsa, kungiyar ta bayyana hakan a cikin kwafin sanarwar manema labaru da suka raba a jiya dauke da sanya hanun shugaban kungiyar Kwamared Aliyu Ladan, inda ya shaida cewar babu wani abu a cikin hakan da ya wuce kokarin cimma manufa ta siyasa, yana mai bayyana cewar babu wani kamshin gaskiya a bisa zargin da ake yi kan Dogara.

Sanarwar ta ce, “Idan za ku iya tunawa, mun nusar da al’umman duniya kan wannan yunkurin da aka shirya na yin zanga-zanga domin a bata wa Dogara suna; mun raba muku takardar manema labaru a ranar 3 ga Yuli, 2018 kan wannan shirin da muka bankado, sai kuma gashi sun gudanar da zanga-zangar su. Na sani mafiya yawan jaridu sun dauka kuma sun shelanta wa duniya manufar hakan, don haka ba mu yi mamaki ba da muka ga matasan nan sun fito suna zanga-zanga, domin tuni mun san da shirin kuma mun fasa musu taya sun kafin su yi,” In ji shugaban.

Kwamared Aliyu ya kara da cewa, naira miliyan 50 ne suka gano aka kashe wajen shirya wannan zanga-zangar, “Wannan zanga-zangar an dauki nauyin gudanar da ita ne daga wasu ‘yan siyasa da suke son cimma wata manufarsu; naira milian 50 aka barnata wajen shirya gangamin zanga-zangar da biyan matasan da suka yi ladarsu domin ba wai sun yi ne don kishin Bauchi ba, bi hasalima babu madogara a ababen da suke fadi; amma an gaza a biya kudin jarabawar WAEC na jihar Bauchi a dalilin haka har yanzu WAEC bata sake jarabawan daliban jihar ba a sakamakon ba a biya ta ba; amma an dauki kudaden an nemo zaune gari banza a biyasu don su yi zanga-zanga,” A cewar sanarwar.

Sanarwar ta kuma kara da bayyana cewar Dogara dan jihar Bauchi ne ta kowace fuska, don haka masoyin jihar Bauchi ne a kowani lokaci.

A bisa haka ne kungiyar ta bayyana cewar an kimtsa cewar idan Dogara ya zo Bauchi za a kai masa hari don haka ne suka jawo hankulan bangarorin jami’an tsaro da su tashi tsaye domin dakile hakan, “Wani sabon shiri yanzu da aka kimtsa, an shirya za a kai wa Dogara hari idan ya zo jihar Bauchi domin jajanta wa jama’an jihar kan ibtila’in Guguwa da Gobara da ta sami jama’an jihar a kwanaki. Don haka a matsayinmu na matasa masu kishin ci gaban yankinmu muna masu sanar da fannonin jama’an tsaro da su tabbatar da dakile wannan yunkurin,” In ji Kwamared Ladan.

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Sakataren kungiyar ta NEYPF Mr. Bulus Gambo ya bayyana cewar talakawa suna zaban shugabanin ne domin su gudanar da aiyukan da za su taimakesu kai tsaye ba fakewa da karerayi da tayar da tarzoma ba, don haka ne ya bayyana cewar dukkanin shugaban da ya gaza gudanar da aikinsa bai kamata ya ke neman bata ma wani mai niyya mai kyau yunkurinsa ba.

Bulus ya bayyana cewar sun gama gano cewar Yakubu Dogara mutun ne mai son zaman lafiya a amma an bisa da bita da kulli a kowace rana, yana mai shaida cewar shirin da aka kashe makuden kudade wajen shiryawa don bata wa Dogara suna a jihar Bauchi shirin ba zai kai ga nasara ba; domin a cewarsa aiyukan Dogara na alkairi a bayyana ne suke ga jama’an jihar Bauchi.

Daga bisani dai kungiyar mai rajin ganin matasan shiyyar Arewa maso gabas sun samu ci gaba sun jawo hankulan matasa da jami’an tsaro dangane da karatowar lokacin babben zabe, inda suka nemi matasa da su kauce wa biye wa ‘yan barandan siyasa masu hargiza lamari da neman janyo tashin hankali a tsakanin jama’a.

Suka ce, “Dogara shine mutum na hudu a daraja a fadin Nijeriya, kuma jama’an kasar nan sun san irin gudunmawar da yake bayarwa wajen gina kasa. Mutum ne wanda ya kauce wa banbancin addini da kabilanci wajen yunkurinsa na kawo ci gaba wa kasar nan, don haka dukkanin mai shirya zanga-zanga domin bata masa suna yanayi ne a banza domin basu da wata hujja na cewar Dogara ya zaga yin aiyukan da jama’a suka zabesa a kai, sai dai a fake da wasu abubuwan da kawai shaci fadi ne, don haka muna jawo hankulan matasa kan wannan lokacin da ya kamata mu hada kanmu wajen kwato ‘yancinmu daga hanun ‘yan siyasan da suka kasa sakau, kada mu tsaya biye wa ‘yan kwangilar siyasa masu maidamu ‘yan Karen farauta, mu duba shugaban da ya sauke nauyinsa mu karfafeshi domin kara masa kwarin guiwa,” in ji kungiyar ta NEYPF.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!