Connect with us

LABARAI

An Rantsar Da Sakatarorin Din-Din-Din A Yobe

Published

on

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam ya rantsar da sabbin sakatarorin din-din-din tare da wasu manyan jami’an gwamnatin jihar, wanda aka gudanar dashi ranar Talata, a Damaturu babban birnin jihar Yobe.

Sakatarorin, sun kunshi Hajiya Hauwa Sulaima, zuwa ma’aikatar mata, Abdullahi Jawa, ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare, sai Bako Adamu zuwa gidan bakin gwamnatin jihar (Liaison Office) da ke Abuja, sai Mangarima Lawan a ma’aikatar aikin gona.

Sauran sun hada da Musa Jidawa a hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA), da Muhammed Abba a ma’aikatar matasa da wasanni sai Alhaji Bukar Dapchi a ofishin shugaban ma’aikata.

Daga cikin manyan jami’an gwamnati kuma, akwai Audi Mamman, na ma’aikatar filaye da gidaje tare da Malam Abdullahi Bego, babban Daraktan hulda da kafofin yada labarai a ofishin gwamnan jihar Yobe, sai Alhaji Samaila Mai Adamu, matsayin babban Darakta a hukumar kula da kadarorin gwamnati.

Bugu da kari, akwai shugaban hukumar kula da ma’aikatan gwamnatin jihar, Alhaji Gagarau Bizi, tare da Alhaji Maina Bukar, mamba na din-din-din a hukumar “Yobe State Fiscal Responsibly Board”, da Alhaji Umar Geidam mamban din-din-din a hukumar kula da ma’aikata a jihar Yobe.

Wasu daga cikin ayarin da aka rantsar din sun hada da Alhaji Musa Musa, mamban din-din-din a ma’aikatar Teaching Serbice Board, sai kuma Saleh Samanja da Alhaji Tijjani Bukar, a ma’aikatar aikin hajji.

A jawabin Gwamna Gaidam ga sabbin manyan jami’an gwamnatin, ya ce “wannan nadi tare da rantsar da wadannan ma’aikatan gwamnati, wani bangare ne wajen ganin ayyukan gwamnati suna tafiya kamar yadda ya kamata a wannan jiha ta Yobe “.

Har wa yau, Gaidam ya shawarci sabbin wadanda suka sha rantsuwar kama aikin da su kasance masu gaskiya da rikon amana da cika alkawarin da suka dauka, kamar yadda ya ke a dokar aikin gwamnati.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!