Connect with us

MANYAN LABARAI

APC Za Ta Bankado Ragowar ’Yan PDP Da Ke Cikinta

Published

on

Jam’iyyar APC ta fara shirin bankado ragowar ‘ya’yan PDP dake cikinta domin ta tabbatar da an kakkabe su daga hukumomi da sauran bangarorin gudanarwa na gwamnati.

Jam’iyyar ta ce, hakan ne kawai zai tabbatar da canjin da Jam’iyyar APC ke muradin samarwa ga ‘yan Nijeirya.

Shugaban Jam’iyyar, Adams Oshiomhole ne ya fadi haka jiya a Sakatariyar Jam’iyyar, yayin da yake rantsar da Membobin kwamitin gudanarwa mutum 39.

Oshiomhole ya jaddada cewa a shirye jam’iyyar take domin amsar korafi daga ‘ya’yanta na halas wadanda suke ganin ba a kyauta musu ba, amma ba za ta lamunci barin duk wani baragurbi a cikinta ba.

“Oshimhole ya ce; “Muna sane cewa har zuwa yanzu da nake maganar nan akwai ragowar ‘yan PDP a cikin jam’iyyarmu, wadanda kuma suke rike da wasu muhimman mukamai a hukumance. Za mu yi iya kokarinmu wurin ganin mun kakkabe ragowar wadannan mutane daga cikin gwamnati, saboda canji muke son kawowa ba wargi ba.

“Ba wai a Billa a ke gudanar da gwamnati kawai ba. Ana gudanarwa tare da tafiyar da gwmanati ne a hukumomin da ake da su – wannan ya shafi abin da hukumomin ke yi, da irin kokarin da suke yi wurin aiwatarwa. Don haka matukar har wadannan hukumomi suna a hannun mutanen da ko kadan ma basu yi amanna da akidar kawo canji ba, don haka bai kamata mu tsammaci wani abu daga gare su ba.” inji shi

Shugaban na APC ya kara da cewa; “Hakki ne da ya hau kanmu na mu sanar da gwamnatin tarayya cewa, wannan gwamnatin ba ta da wata alaka ta kusa ko nesa da PDP, don haka ya haramtarwa duk wani dan PDP rike babban mukami a hukumomin da suke da matukar amfani.”

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!