Connect with us

LABARAI

Atiku Ya Ragargaji Buhari, Ya Ce Gwamnatinsa Ta Fi Muni Tun Daga 1999

Published

on

Tsohon mataimakin shugaban kasarnan, Atiku Abubakar, ya bayyana gwamnatin Muhammadu Buhari a matsayin gwamnatin da ta fi kowacce cuwa-cuwa, tun dawowar kasarnan tafarkin dimokuradiyya a 1999.

Atiku yana magana ne a Abakaliki ranar Talata lokacin da yake wa magoya bayan Jam’iyyar PDP jawabi a sakatariyan gwamnatin Jihar Ebonyi.

Atiku ya isa Jihar ne a ci gaba da yakin neman takarar shugabancin kasarnan a tutar PDP.

“Abin da ke faruwa a kasarnan yanzun, ya saba wa duk wasu tanade-tanade na tsarin mulkin mu. A matsayin tarayya, kamata ya yi a ce muna da gwamnatin da take damawa tare da kowa, kun kuma san wannan gwamnatin ba ta tafiya tare da kowa da kowa.

“Kun kuma san kan wannan gwamnatin ba a hade yake ba, kun ma san sam wannan gwamnatin ba ta cancanta ba, haka kun san ba a yi gwamnatin da ta kai wannan cuwa-cuwa ba, tun bayan dawowarmu tafarkin dimokuradiyya a shekarar 1999.

“Don haka, kar ku bari wani ya zo ya yaudare ku da batun yakar cin hanci da rashawa, sun fi kowa cin hanci da karban rashawa, da sannu kuma za mu yi ta tona masu asiri.

“Rashin ayyukan yi kullum sai kara hauhawa suke, ba a kuma taba samun wani lokaci ba a kasarnan da aka kori matasanmu maza da mata har milyan 11 daga wuraren ayyukansu.

“Maganan da nake da ku a yanzun, akwai matasan da ba su da aikin yi a kasarnan sama da milyan 11. Sha’anin tsaron kasarnan ya tabarbare. Duk wani abin bukata na yau da kullum ya yi tashin gwaron zabi, duk a sakamakon wannan karkatacciyar gwamnatin ta APC,” in ji Atiku.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!