Connect with us

LABARAI

Gamayyar PDP: Taron ‘Yan Neman Sa’a Ne Da Son Mulki Ido Rufe – Balarabe Musa

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji AbdulKadir Balarabe Musa, ya ce, sanya hannu a yarjejeniyar fahimtar juna da jami’yyar PDP tare da wasu jam’iyyu 39 suka yi don tunkarar babban zaben shekarar 2019, gamayya ce ta ‘ yan neman sa a da masu neman mulki ido rufe.

Balarabe Musa ya yi wannan bayanin ne a tattaunawarsa da ‘yan jarida a Abuja ranar Talata.

Ya ce, “Bana tunanin gamayya irin wannan nan ‘yan neman sa at zasu iya kayar da jam’iyya mai mulki ta APC.”

Kanfanin Dillacin Labarai na kasa NAN, ya ruwaito cewa, jam’iyyar PDP dana SDP da kuma wasu jam’iyyu 37 da kuma wasu kugiyoyi sun sanya hannu a wata yarjejeniyar hadin kai don fuskantar zaben shekarar 2019.

Shugabannin jam’iyyun na kasa ne suka sanya hannu a kan takardar yarjejeniya inda suka yi alkawarin aiki tare a karkashin tutar “Coalition for United Democratic Parties (CUDP)’’ da nufin fitar da dan takarar shugabancin kasa daya a zaben dake tafe.

Alhaji Balarabe Musa wanda kuma shi ne shugaban jamiyyar PRP, ya ce, jam’iyyarsu bata cikin wanna hadaka da jam’iyyar PDP ke shugabanta.

“Ya kamata ka tuna cewa, babba dalilin haduwarsu shi ne don sun daman shiga tsarin rarraba mukami tsakaninsu, shi ne kawai yasa suka yi wannan hadakar don samun mukami kawai.

“Ba wai suna bukatar gudanar da aiyyuka ga alummar Nijeriya bane, ba wai don abin da jamiyyar APC ta kasa yi bane ba kuma saboda banbancin akida bane.

“Babu wani gaggarumin banbanci tsakaninsu da jamiyyar APC, wasu gungun ‘yan siyasa ne masu bukatar kayar da jamiyyar APC bana tunanin wannan hadakar zata iya kawar da APC,”inji shi.

Ya kara da cewa, abin da ake bukata shi ne, hadakar da zai bayar da karfi a bangaren akidar data fi ta jamiyyar APC ba wai maganar harurfofin APC kawai ba.

“Wannan hadakar ba zasu samar da wani banbanci ba, bana tunanin zasu samu nasarar abin da suka sa a gaba.

“Tsakanin yanzu zuwa watan Augusta zamu fahinci ko zasu samar da ingantacciyar canjin sa APC ta kasa samarwa” inji shi.

A kan zaben shekarar 2019, Balarabe Musa ya ce, a halin yanzu kan ‘yan Nijeriya ya waye don kuwa ‘yan Nijeriya na bukatar shugabanci ne mai inganci.

“Ya kamata mu sani cewa, a kwai hanyoyi da daman gaske da za a iya hada kan ‘yan Nijeriya ta hanyar hadadiyyar akida da hadin kan kasa da kuma bunkasa daukacin Nijeriya gaba daya.

“Na biyu kuma dole mu tabbatar da an samu yin zabe ba tare da nagudi ba ta hanyar samar da karbabbiyar gwamnati.

“Na uku kuma dole a gaggauta tsayar da sace sace da barnatar da dukiyar al’umna da ake tafkawa ba tare da wani bata lokaci ba.

“In har aka kasa yin wani abu don gyara halin da ake ciki al’amarin zai ci gaba da lallacewa, dole mu gyara lamarin ta hanyar yin gyara ga tsarin mulkin kasar nan in kuwa bamu yi wani abu ba to mu shirya fuskatar matsaloli masu yawa a nan gaba.

“A halin yanzu bangaren zartaswa da bangaren dokoki suna fada da juna, suna kuma wannan fadan ne tun daga farkon wannan mulkin a shekarar 2015, dole a kawo karshen wannan fadace fadacen,” inji shi.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!