Gwamnatin Tarayya Za Ta Rufe Gadar ‘Third Mainland’ Ta Legas Domin Yin Gyara — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rufe Gadar ‘Third Mainland’ Ta Legas Domin Yin Gyara

Published

on


Bayanai suna nuna cewa, kwanan nan gwamnatin tarayya za ta bayar da umurnin rufe babbar gadan nan na ‘Third Mainland Bridge’ don fuskantar gyara sakamakon lallacewa da ya yi.

Jami’in gwamnatin tarayya mai kula da aiyyuka a Legas, Adedamola Kuti ne ya bayyana haka ranar Talata a garin Legas, ya kuma ce, ana ci gaba da tattaunawa don kulle gadar kwanan nan. Ya kara da bayyana cewa, ma’aikatar aiyyuka za ta yi taro na musamman da masu ruwa da tsaki ranar Laraba domin tattauna yadda za a sarrfa zirga zirgan motoci  tsakanin gadar da kuma bangaren ‘Mainland’ inda yawancin manyan kanfanoni da hukumomin gwamnatin kasar nan keda ofishoshisu.

Ya ce, ana sa ran kulle gadar ne daga karfe 12 na daren Alhamis don yin gwaje gwaje da gyare gyaren da za a yi, za a kuma bude gadan da misalin karfe 12 na dare ranar Lahadi.”

Duk da cewar bai bayyana takamaima lokacin da za a rufe gadar gaba daya ba bai kuma bayanin tsawon lokacin da gyaran zai dauka ba, amma dai jama’a nada da tabbacin cewa kwanan nan nan za a fara aikin gyara gadan.

Masu ruwa da tsakin da ake saran zasu samu halartar taron da za a gudanar a kan gyaran gadan sun hada da kungiyoyin direbobi da kungiyar masu manyan motoci da kuma jami’an tsaro.

Majalisar zartaswa ta tarayya ce ta amince da kashe Naira Biliyan 18.874 domin gyara da inganta gadan, an kuma ba kanfanin kasar Italiyan nan ne mai suna Borini Prono, wanda sune suka gina gadan tun da farko.

“Tuni aka fagudanar da aikin, a yayin da muke gudanar da aikin daga lokaci zuwa lokaci dole zamu rinka dakatar da amfani da gadan,´inji Kuti

“A halin yanzu zamu fara gudanar da gwaje gwaje a kan gadan, saboda haka muna saran zamu kulle gadan daga 12 na dare ranar Alhamis don gudanar da gwaje gwaje zuwa tsakar daren ranar Lahadi.”

Kuti ya kuma ce, wasu gadoji guda 6 a fadin jihar da suka lallace suna fuskantar gyara daban daban.

Ya bayyana cewa, an fara gudanar da gwaje gwaje a kan ‘Otedola Bridge’,wanda motar tankan mai ta kone a kansa, ya ce, gwaje gwaje sun nuna gadan nada cikkaken ingancin da motoci zasu iya wuce wa ta kansa ba tare da wani fargaba ba.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!