Juventus Tana Zawarcin Marcelo Bayan Ronaldo — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Juventus Tana Zawarcin Marcelo Bayan Ronaldo

Published

on


Rahotanni daga kasar Italiya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Jubentus tana zawarcin dan wasan baya na kungiyar  kwallon kafa ta Real Madrid, Marcelo, dan kasar Brazil domin yakoma kungiyar.

A ranar Talata ne dai kungiyar kwallon kafa ta Jubentus ta kammala siyan dan wasa Ronaldo daga kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid akan kudi fam miliyan 105 wanda hakan yakawo karshen zaman shekaru 9 da dan wasan yayi a kungiyar.

Kungiyar kwallon kafa ta Jubentus dai tana ganin samun Ronaldo zaisa Marcelo shima yayi tunanin barin kungiyar domin sake hadewa da ronaldo wanda sukayi shekara da shekaru a kungiyar.

Marcelo, mai shekaru 30 a duniya ya buga wasanni sama da 450 a kungiyar bayan yakoma kungiyar daga kungiyar kwallon kafa ta Carringtian dake kasar Brazil.

Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Jubentus tana bukatar siyar da wasu daga cikin ‘yan wasanta idan har tanason sake siyan dan wasa mai tsada.

Abune mai wahala kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta yarda ta siyar da daya daga cikin manyan ‘yan wasanta wanda take tunanin babu kamarsa kawo yanzu sai dai watakila dan wasan ya bukaci shima kungiyar ta siyar dashi.

Marcelo dai ya wkilci Brazil a gasar cin kofin duniya wanda ake bugawa yanzu haka  a kasar Rasha

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!