Connect with us

LABARAI

Kunguyar KSI Na Son Kwankwaso Ya Tsaya Shugabancin Kasa

Published

on

An bukaci Sanata mai wakilkar Kano ta Tsakiya, tsohon gwamnan jihar Kano, (Dr) Rabiu Musa Kwankwaso ya tsaya takarar shugabancin kasar nan zaben shekarar 2019. Kungiyar da aka sani da Kwankwaso Support Initiative (KSI) ta yi kira ne a wata sanarwa da Shugabanta, Abdullahi Dahiru Esq da Sakatare, Franklin Onyeneke, a wata sanarwa da suka baiwa manema labarai a garin Abuja.

KSI ta bukaci Sanata Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ya tsaya takarar neman shugabancin Tarayyar Nijeriya.Sun tabbatar masa da cewa kungiyar su a shirye take ta bashi dukkan wani goyan baya da yake bukata.

Kungiyar ta yi la’akari da cewa Kwankwanso ya yi takara da  ‘yan takara na Jam’iyyar APC, tare da shugaba Muhammadu Buhari da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, inda ya zo na biyu tare da kuri’un kuri’un 974 da suka gudana har zuwa zaben 2015.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!