Majalisar Dokokin Neja Za Tai Doka Kan Bangar Siyasa — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

Majalisar Dokokin Neja Za Tai Doka Kan Bangar Siyasa

Published

on


An yabawa jam’iyyar APC kan yadda ta gudanar zaben shugabannin jam’iyyar daga makin mazaba zuwa kananan hukumomi, jiha da tarayya ba tare tashin hankali a duk fadin kasa ba. Dan majalisar dokokin jiha mai wakiltar karamar hukumar Rafi, Hon. Muhammad Danlami Bako ne ya yi yabon a ofishin sa da ke majalisar Rt. Hon Usman Jikantoro da ke minna.

Hon Danlami Bako ya cigaba da cewar lallai yadda aka gudanar zaben abin a yaba ne, sai dai ya janyo hankalin wadanda ba su ji dadin yadda zabukan suka gudana da su kai koken su inda ya kamata, domin mu a jihar Neja mai girma gwamna ya umurci jam’iyya da ta kafa kwamiti a dukkanin kananan hukumomi ta yadda za a samu damar sauraren korafe-korafen jama’a da hanyar da za a bi wajen magance su.

Dan majalisar yace yanzu haka a kokarin majalisar na dakile bangar siyasa a jihar, tana gabatar da doka kan bangar siyasa. Don haka yana jawo hankalin ‘yan siyasa musamman ‘yan APC da su zama masu bin doka da oda, domin da zaran an gabatar da dokar lallai duk wanda ya bari ya fada komon ‘yan bangar siyasa zai fuskanci hukuma.

Don haka ina goyon bayan maigirma shugaban kasa, Muhammadu Buhari na kowa halinsa ta fishshe shi, domin abinda ke haddasa bangar siyasa rashin gaskiya da son murdiyar zabe.

Idan mutumin da aka zaba bai yiwa jama’arsa komai ba sai ya koma ya zauna domin bai da abin nunawa, canjin da aka yi a kasar nan shi din ne ya baiwa gwamnati samun damar ayyukan da ta ke yi a halin yanzu. Ina kiran al’ummar kasar nan da jihar Neja da su kuri’arsu ita ce za tai hukunci a zabe mai zuwa, wajibin mu ne mu wayar da kan jama’a muhimmancin mallakar katin zabe, domin shi ne kawai zai ba su damar yanke hukunci ga shugabanni masu zuwa.

Danlami Bako yace kafin karewar wa’adin wannan majalisar zasu tabbatar sun yi dokoki masu anfani ga jiha da kuma al’ummar kasar nan.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!