Real Madrid Ta Yi Kuskuren Siyar Da Ronaldo –ZIDANE — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Real Madrid Ta Yi Kuskuren Siyar Da Ronaldo –ZIDANE

Published

on


Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta tabbatar da kammaluwar cinikin Cristiano Ronaldo zuwa Jubentus bayan da aka ga shugaban kungiyar kwallon kafa ta Jubentus Andrea Agnelli ya kai ziyara masaukin Cristiano Ronaldo da ke birnin Kalamata a kudancin Girka.

Babu tabbacin abin da suka tattauna tsakaninsu yayinda bayan sa’o’I kalilan bangarorin biyu suka sanar da kammaluwar cinikin

“Zan iya cewa sunyi kuskuren siyar dashi saboda ba a wannan lokacin yakamata kungiyar ta rabu dashi ba kuma kafin siyar dashi akwai bukatar akawo manda zai maye gurbinsa ko kuma a samu tabbacin wanda zai maye gurbin nasa” cewar Zidane

Yaci gaba da cewa “A yanzu kuma akwai aiki a gabansu na nemo wanda zai maye gurbinsa kuma abune mai wahala a samu sai dai a hankali wanda aka siyo zai kai matsayin da Ronaldo din yakai”

Tun farko Ronaldon wanda ya lashe kyautar Balon d’Or har sau biyar shi da kansa ya nuna bukatar komawa Jubentus din kan Yuro miliyan 88.

Kammaluwar cinikin dai ya kawo karshen shekaru 9 da Ronaldo ya shafe a Real Madrid tun bayan sayo shi daga Manchester United kan Yuro miliyan 80, inda ya zamo mafi zura kwallo a raga a tarihin kungiyar bayan da ya zura mata kwallaye 451.

A iya zamanshi a Madrid, Ronaldo dan Portugal mai shekaru 33 ya dage kofunan Laliga 2 Copa del Rey 2 da na zakarun Turai guda 4.

Tuni dai Christiano Ronaldo ya wallafa sakon tafiyar ta sa, inda ya ce lokaci ya yi da zai fara sabuwar rayuwa.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!