Real Madrid Ta Yi Min Komai A Rayuwa Ta –Ronaldo — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Real Madrid Ta Yi Min Komai A Rayuwa Ta –Ronaldo

Published

on


Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tayi masa komai  a rayuwarsa kuma bazai taba mantawa da kungiyar ba a rayuwarsa.

A ranar Talata ne dai kungiyoyin Real Madrid da Jubentus suka amince da cinikin dan wasa Ronaldo zuwa kasar Italiya akan kudi fam miliyan 105 wanda hakan yakawo karshen shekara tara  dan wasan yayi a Real Madrid.

Kafin tafiyarsa dai Ronaldo ya kasance dan wasan dayafi kowanne dan wasa zura kwallo a kungiyar bayan daya zura kwallaye 450 cikin wasanni 430 daya buga a kungiyar tun bayan komawarsa daga Manchester United a shekara ta 2009.

“Shekarun danayi a Real Madrid da kuma birnin Madrid bazan taba mantawa dasu ba a rayuwa domin shekaru ne na farin ciki da bazan taba mantawa dasu ba a rayuwa ta babu abinda zan iya cewa a halin yanzu sai dai godiya da fatan alheri ga kungiyar” in ji Ronaldo.

“Lokaci yayi daya kamata in bar Real Madrid saboda haka yasa na tambayi kungiyar cewa tabani dama in bar kungiyar kuma suka amince da hakan kuma ina godiya da amsa bukata ta”

Kungiyar kwallon kafa ta Jubentus ta amince zata bawa Ronaldo fan dubu dari biyar a matsayin albashi idan yakoma kungiyar inda tuni dan wasan ya kammala amince kuma zai saka hannu a yarjejeniyar shekaru biyar.

 

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!