’Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Sakkwato — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

LABARAI

’Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Sakkwato

Published

on


Wasu mahara sun kai wani mummunan farmaki a kauyan Tabanni, da ke karamar hukumar Rabah, ta Jihar Sakkwato, a ranar Talata, inda suka kashe dagacin garin, Usman Mohammed, da kuma wasu mutanan guda 45.

Wata tabbatacciyar majiya daga kauyan ta bayyana cewa, maharan da ke dauke da bindigogi sun kuma kone kauyan kurmus, sannan kuma suka bi al’umman kauyan da ke gudun ceton rai da harbin kan-mai-uwa-da wabi.

Majiyoyi daban-daban da suka hada da babban dan dagacin kauyan da aka kashe, Aliyu Ibrahim, duk sun tabbatar da kai harin, wasunsu ma cewa suka yi sun kirga gawarwaki 50 a asibitin na Gandi.

Da farko maharan sun cinna wa kauyan wuta ne, sai kuma suka bi mutanan da ke kokarin tserewa wutar da harbi.

“Yanzun garin ba kowa cikinsa. Wadanda suka yi sa’ar tsira daga farmakin yanzun suna gudun hijira ne a garin Gandi,” in ji Iro Aminu, wanda shi ma ya sami tsira daga farmakin.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Sakkwato, Cordelia Nwawe, ta tabbatar da kai harin, sai dai ta ce, rundunar ba ta tabbatar da yawan mutanan da suka mutu a harin ba a halin yanzun.

“Yanzun komai ya lafa, za mu fitar da sanarwar cikakken bayanin abin da ya faru zuwa gobe,” in ji ta.

Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!