Connect with us

LABARAI

Akwai Alaka Mai Karfi Tsakanin Gwamnatin Kaduna Da ‘Yan Jaridu –Saidu Adamu

Published

on

An bayyana irin gagarumin gudunmuwar da ‘yan jaridu ke ba Gwamnatin Jihar Kaduna, a matsayin abin a yaba masu ne, musamman idan akayi la’akari da yadda zaman lafiya da kwanciyar hankali ya samu karbuwa da kuma karuwa a fadin jihar.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Babban mai ba Gwamnatin Jihar Kaduna shawara na musamman akan harkokin yada labarai da kuma sadarwa, Honorabul Saidu Adamu, a lokacin da ya yi wani zama na musamman da Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen Jihar Kaduna, a Sakatariyar kungiyar dake Kaduna.
Saidu Adamu, ya bayyana cewar, Gwamnatin Jihar Kaduna, na sane da irin dimbin gudummuwar da kafafen yada labarai suke bayarwa wajen ganin an sami daidaito tsakanin gwamnati da kuma al’ummar jihar Kaduna, musamman ma a bangaren da ya shafi harkokin tsaro, kiwon lafiya, harkar ilimi, da dai sauran su.
Ya kara da cewar, “Dalilin kawo ita wannan ziyara shi ne, domin na kara kulla daukon zumuncin dake tsakanin Gwamnatin Jihar Kaduna, da kungiyar ‘yan jaridu ta kasa reshen wannan jiha ta mu ta kaduna, domin bayyana masu godiyar Gwamnan Jihar kaduna a gare mu a bisa irin namijin kokarin da suke nuna wa a yayin gudanar da aiyukansu a fadin wannan jihar.”

“Ina mai tabbatar maku da cewar, Gwamnatin Jihar kaduna a shirye take da ta ci gaba da yin aiki kafada da kafada da kafafen yada labarai dake aiki a wannan jihar, domin ganin sun ci gaba da bayyana ma al’ummar wannan jihar irin dimbin ayyukan ci gaba da Gwamnatin Malam Nasiru El-rufai take yi.”

Mai ba gwamnan shawara akan harkokin yada labarai da sadarwa, ya ci gaba da bayyana cewar, “ duk da a wani lokaci akan samu wasu batagarin ‘yan jarida na rubuta labarai marasa inganci na kage da kuma sharri, akan wannan gwamnati, domin kawai su tayar da zaune tsaye a wannan jihar, wanda kuma tsakani na da Allah gwamnati ba za ta yarda da irin wannan hali na bayyana labaran karya da wasu ‘yan jarida ke yadawa ba. Domin zaman lafiya shi ne babban burin wannan gwamnati, kuma duk wani wanda ya ce, zai kawo tangarda tsakanin gwamnati da zaman lafiya, to tabbas doka ba za ta barshi ba.”

Daga karshe ya roki ‘yan jaridu da cewar, su daina barin wasu batagarin ‘yan siyasa na amfani da su, domin ganin sun cinma wani burinsu a siyasan ce, wanda hakan ba karamar barazana ba ce ga kuma tafiyar hawainiya , ga mulkin dimokaradiyar kasar nan, domin a cewarsa, Dan jarida daya na iya rubuta labarin karya na kage guda daya tilo, amma daga karshe a samu asarar dimbin rayuka da kuma dukiyoyin al’umma
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!