Connect with us

LABARAI

An Nada Sabon Shugaban Majalisar Dokokin Filato

Published

on

Majalisar Dokoki ta Jihar Filato ta yi sabon shugaba wanda aka nada kuma shi ne Honarabul Johua Madaki dan Majalisar da yake wakiltar karamar hukumar Jos ta gabas.
Nadin Hon Johua Madaki, ya biyo bayan tsige shugaban majalisar Mr Peter Azi, wanda tun makonni biyun da suka gabata ‘yan majalisar suke kokarin tsige shi akan dalilan rashin iya tafiyarda harkokin majalisar.
Mataimakin shugaban majalisar Dokokin Hon Saleh Yipmong, ne ya shugabanci zaman majalisar bayan tsige kakakin kuma ya bukaci majalisar da ta gabatar masa da wanda za’a zaba saboda maye gubin da shi shugaban majalisar ya bari, inda tsohon mataimakin kakakin majalisar Hon. Yusuf Gandi, daga mababar Kantana a cikin karamar hukumar Kanam, ya bada sunan Hon. Joshua Madaki daga karamar hukumar Jos ta gabas, wanda dukkan yan majalisan su kayi na’am dashi suka amince gabadayan su, bayan haka ne kuma nan take sai aka rantsar dashi.
Mr. Peter Azi,an tsige shi ne a wani zaman da suka yi ranar Laraban ta wannan makon da muke ciki, inda wakilai 20 daga cikin 24 na majalisar suka amince da a tsige shi, aka kuma mika masa takardar da suka sa hannun tsigeshi daga kan mukaminsa na shugaban majalisar, wanda daya daga cikin ‘yan majalisar Hon Peter Gyandeng na jam’iyyar PDP, daga karamar hukumar Barakin Ladi, ya mika masa takardar tilasta masa ya sauka daga kan mukaminsa na shugaban majalisar.
Hakanan kuma a zaman da ‘yan-majalisar suka yi ranar Laraba sun tsige shugaban masu rinjaye na majalisar [majority leeder], Henry Yinkwap, inda wakilai 12, daga cikin 17, na Jam’iyyar APC mai mulki a jihar, suka sa hannu zabenn Nanlong Daniel Mikan, a matsayin wanda zai maye gurbinsa.
A jawabainsa na kama aiki sabon Kakakin Majalisar Hon. Joshua Madaki ya’yi alkawarin yin aiki sai inda karfin shi ya kare, don inganta ayyukan majalisar kamar yadda al’ummar jihar suke bukata
Shima da yake sa albarkacin bakin shi akan al’amarin tsige shugaban majalisar Hon, Ibrahim Baba Hassan, wanda yake walkiltar mazabar Arewa daga karamar hukumar Jos ta Arewa, ya nuna rashin jin dadinsa bisa tsarin da aka bi na tsige shi kakakin majalisar, inda ya ce dama ambashi dama ya sauka daga mukamin .
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!