Burina In Yi Fice Fiye Da Wizkid Da Davido A Fagen Waka – Aminu Real Boy — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

BIDIYO

Burina In Yi Fice Fiye Da Wizkid Da Davido A Fagen Waka – Aminu Real Boy

Published

on


Ismail Aminu wanda aka fi sani da ‘Real Boy’, Karamin Yaro ne Dan kasa da shekara goma 11 haihuwa, wanda ya hore ma basirar iya wakar zamani, wanda a turance ake kira da Hip Hop, kuma an haife shi a shekarar 2007, a Karamar hukumar Kaduna ta Arewa, da ke Jihar Kaduna.
Ismail Aminu (Real Boy), ya yi fice sosai a fannin rubuta wakokin Turanci da Hausa zamani wato Hip Hop, sannan ya shara wajen iya yin rawa fiye da yadda ake zato. A halin yanzu ya sami nasarar raira wakoki masu tarin yawa a karkashin Kungiyar Matasan nan da ake kira Dynamic Arewa Empire, dake kaduna.
Masana masu yin sharhi akan Al’amuran da ya shafi rawa da waka, sun bayyana Ismail Aminu (Real Boy) a matsayin Matashin mawakin da a halin yanzu tauraronsa ke haskawa tun bayan rasuwar hazikin mawakin nan Lil Ameer, dake Jihar Kano, domin a cewarsu, a halin yanzu Manya da Kananan Mawaka na ta hadakar zawarcin Yaron domin ganin sun yi waka a tare da shi.
A tattaunawar da ya yi da wakilinmu, Ismail Aminu (Real Boy), ya bayyana ma wakilinmu cewa, burinsa shi ne ya ga cewa ya daukaka a fage waka fiye da mawakan nan na Kudancin kasar nan, wato Wizkid ko Dabido. Sannan ya kara da bayyana cewa, babban burinsa a rayuwarsa bai wuce a ko da yaushe ya ga yana taimaka ma marasa galihu da kuma marayu.

Advertisement
Click to comment

labarai