‘Daga Juventus Ronaldo Zai Yi Ritaya’ — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

‘Daga Juventus Ronaldo Zai Yi Ritaya’

Published

on


Wakilin dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Jubentus, Jorge Mendes ya ce dan wasan zai kammala buga kwallo a kungiyar kwallon kafa ta Jubentus bayan kwantaraginsa ya kare a kasar ta Italiya.
A wannan satin ne dai Ronaldo ya kammala komawa kungiyar kwallon kafa ta Jubentus bayan ya shafe shekaru tara a Real Madrid inda ya lashe kofuna da dama da suka hada da laliga guda biyu.
Har ila yau Ronaldo ya lashe kofin Copa Del Rey guda biyu da kuma kofin zakarun turai guda hudu bayan kuma ya kasance dan wasan dayafi zura kwallo a raga da kwallaye 450 a wasanni 438 daya buga a Real Madrid.
“Nayi farin ciki da Ronaldo yace Jubentus ce kungiyar sa ta karshe a duniya kuma wannan mataki daya dauka yayi dai dai ganin yadda ya kafa manya manayn tarihi a rayuwarsa’ in ji wakilinsa Mendes
Yaci gaba da cewa “ Ina godiya ga shugaban kungiyar Jubentus, Andrea Agnelli bisa bajintar daya nuna na zuwa ya tattauna da Real Madrid akan siyan Ronaldo sannan shima manajan kungiyar Beppe Morotta bisa nuna kwarewa da yayi a yayin tattaunawar”
Real Madrid dai ta biya biya fam miliyan 80 a lokacin data siyi Ronaldo daga Manchester United a ashekara ta 2009 sannan kuma yanzu ta karbi fam miliyan 105 daga hannun Jubentus.
A ranar hudu da watan Agusta mai kamawa ne Jubentus zata kara da Real Madrid a wani wasan sada zumunta a birnin Amurka.

Advertisement
Click to comment

labarai