Fafatawar Matsayi Na Uku: Ko Ingila Za Ta Fanshe Haushinta? — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Fafatawar Matsayi Na Uku: Ko Ingila Za Ta Fanshe Haushinta?

Published

on


Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Edin Hazard, wanda kuma yake wakiltar kasar Belgium a gasar cin kofin duniya ya bayyana cewa wasansu da Ingila a wasan neman zama na uku a gasar cin kofin duniya ba mai sauki bane sai dai akwai bukatar su zama na uku a duniya.
Hazard, wanda kasarsa ta sha kashi a hannun kasar Faransa a wasan kusa dana karshe na gasar cin kofin duniya ya bayyana cewa basuji dadin rashin zuwa wasan karshe ba saboda sun cancanta dasuje wasan karshe amma kuma idan suka dage suka zama na uku zasu samu sauki.
Belgium dai zata fafata da kasar Ingila a wasan neman na uku a gasar cin kofin duniya wanda akeyi a kasar Rasha bayan itama kasar Ingila tasha kashi a hannun kasar Crotia daci 2-1 a wasan da suka fafata a ranar Laraba.
Kasashen biyu dai sun hadu a cikin rukuni na H a gasar sai dai a karawar da sukayi kasar Belgium ce tasamu nasara daci 1-0 ta hannun tsohon dan wasan Manchester United, Adnan Januzaj.
Sai dai za’a iya cewa a wasan da suka fafata kowacce kasa ta ajiye manyan ‘yan wasanta saboda wasa na uku suka buga kuma na karshe a rukunin bayan da tun farko kasashen biyu suka samu fitowa daga cikin rukunin bayan sun samu maki shida-shida a rukunin daya hada da kasashen Panama da Tunisia daga nan nahiyar Africa sai kuma kasar Ingila da Belgium wadda tayi na daya a rukunin.
Rabon kasar Ingila da buga wasan neman na uku tun a shekarar 1990, gasar cin kofin duniyan da aka fafata a kasar Italiya kuma Ingilan tasha kashi a hannun mai masaukin baki Italiya daci 2-1.
Itama kasar Belgium sau daya ta taba zuwa wasan neman na uku a shekarar 1986 sai dai tayi rashin nasara a hannun kasar Faransa a gasar da aka buga a kasar Medico.
Dukkanin kasashen dai sun buga wasa mai kyau a a gasar wadda take gudana a kasar Rasha sai dai burinsu na zuwa wasan karshe yazo karshe bayan da sukayi rashin nasara a hannun kasashen Faransa da Crotia.
A gobe Asabar za’a buga wasan da misalin karfe uku agogon Nijeriya a filin wasa na Saint Petersburg da ke kasar Rasha. Shin ko Ingila za ta fanshe haushinta a kan nasarar da Belgium ta yi a kanta a wasan rukuni tun farkon gasar? Masu magana dai kan ce “ba a san maci-tuwo-ba-sai-miya-ta-kare”!

Advertisement
Click to comment

labarai