Connect with us

Madubin Rayuwa

Girki Adon Mace: Yadda Ake Kunun Zaki Na Gero Da Alale

Published

on

• Nigerian Moi Moi _ How to Make Nigerian Moi Moi
Wannan karon filinmu zai yi magana ne akan kalolin girke girke. Wasu mata basa damuwa da ba da lokacinsu wurin girki , ko neman sabbin hanyoyin sarrafa abinci na yau da kullum. Wata mace idan ta rike girki daya sai tayi wata guda shi ta ke sarrafawa, daga nan maigida sai ya fara neman wani kalar abinci a waje shikenan an samu hanyar samar da matsaloli a wannan gida.
Yana da kyau mace ta fahimci wani irin abinci maigida yafi bukata? Yara ma me sukafi bukata ?sai ta tsara lokaci yadda zatayi girke girkenta ba tare da ta samu matsala ba. Sannan a lokacin hutun maigida kamar ranakun juma’a, asabar, lahadi da mafi yawan magidanta kan samu lokacin zama cikin iyalansu to yana da kyau mace ta samar da samfurin abinci da abinsha don burge iyalanta.
Ba kuma jin haka yasa mace kai kanta inda Allah bai kaita ba, har kullum ina bayar fa shawarar yin amfani da abinda bai fi karfinmu ba. Sannan mace idan ta fahimci maigida ma’abocin ci ko shan kayan gwangwani ne ta bashi shawara tare da jajircewa wurin sarrafa abinci da abinsha na daga abubuwan da muke nomawa kuma muke dashi yafi. Hakan zai taimaka wurin rage kashe kudi da samun ingantaccen lafiya. Zanyi magana ne akan abu biyu kawai na abinci da abinsha daga abinda muke da shi.

KUNUN ZAKI NA GERO
Abin bukata
Gero
Dankalin hausa
Danyar citta
Kananfari
Sugar
Flabour na kwakwa
Da farko zaki jika gero, idan ya jika sai Ki wanke, ki samu dankalin hausa kadan ki bare bayan Ki yanka akan geron sai ki sa citta da kananfari a markada. Bayan an markada Ki tace shi da abin tata, idan ya kwanta ki dora ruwan zafi akan wuta idan yayi zafi sosai sai ki juye akan kullin gero da dankalin nan, kiyi ta gaurayawa idan ya huce sai ki saka flabour na kwakwa da sugar kina iya kara zuba danyar citta da kananfari idan kamshin baiyi miki yadda kike so ba. Sai a zuba a fridge idan yayi sanyi a sha.
A kula shi irin wannan hadin kunun zaki ana yinsa ne iya adadin da za a iya shanyewa a wuni saboda gudun kar yayi tsami ko ya baci.
Alale (moi-moi)
Shi wannan alale ana samar dashi ne ta wake, duk da akwai samfurin alale Kala -kala da kuma yanayin yadda ake yinsa. Shi wannan alale ana yinsa ne da leda ba gwangwani ko robobi ko wani abu dabam ba.
Abin bukata :
Wake
Attaruhu /tattasai /albasa
Kifi
Mangyada
Curry
Maggi/gishiri.
Leda.
Da farko bayan kin wanke wake kin tabbatar kin cire dusar da ke jikin waken sai Ki wanke waken da kyau. Ki saka attaruhu da tattasai kadan kadan hade da albasa. Ki kai markade ko ki markada a blender. Ki samu danyen kifi ki wanke sosai da lemon tsami ko gishiri, in kin tabbatar karnin ya fita sai ki zuba curry da magi ki tafasa sama -sama sai ki soya kifin. Idan markade ya dawo sai ki zuba kayan dandanon banda gishiri maggi ya wadatar, ki yanka isasshen albasa, Ki zuba mangyada, sai ki dauko soyyayen kifin nan ki zuba cikin markaden ki gauraya sosai, Ki saka ruwa kadan idan kina da bukata kina iya fasa danyar kwai Ki zuba ko kiyi da danyar kwai maimakon kifi. Ki yi zubawa a leda kina kullawa, kafin nan kin dora ruwan zafi a murhu sai ki zuba kullalen markaddaden wake mai hadin nan ta yadda kowani daya zai sake cunkusuwarsu sai sa su kin nuna ko ayi ta daukar wani ya gefe ya nuna wani gefe bai nuna ba. Idan ya nuna kamshi zai yi ta tashi sai ki sauke. Mafi aksarin irin wannan alale baya bukatar miya ko yaji sai ayi sarbing din magida da yara.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!