Connect with us

LABARAI

Gwamnatin Nasarawa Ta Kaddamar Da Yaki Da Cin Zarafin Yara

Published

on

Gwamnatin jihar Nasarawa ta kaddamar da wayar da kan al’umma dangane da yaki da cin zarafin yara domin kyautata wa marayu da marasa galihu rayuwarsu tare da kare su daga fadawa hannun miyagu masu gurbata masu rayuwa.
Ma’aikatar hakkokin mata da ci gaban matasa ta jihar Nasarawa tare da fannonin jami’an tsaro da kuma ma’aikatar shari’a ta jihar, kungiyoyin fararen hula guda10, sai kuma sashen walwala da jin dadin jama’a na kananan hukumomi 10 daga cikin 13 na jihar sune ake sa ran za su jagoranci gudanar da wannan gangami na yaki da cin zarafin yara, mai taken “End Biolence Against Children (E-BAC) Multi-Sectoral Response Plan”, wato ‘’Gangamin kawo karshen cin zarafin da ake yi ma yara’’ ana sa ran za su fara aiki gadan-gadan ne a farkon watan Agusta mai kamawa nan da kwanaki.
Babban sakatare a ma’aikatar harkokin mata da ci gaban yara Asibi Omeri Ogabo, ta bayyana damuwarsu matuka akan yadda ake cin zarafin yara a wannan zamanin.
Ta ce, “Yara suna rayuwa ba tare da kulawar iyayensu ba; wanda kuma wannan al’amarin hakki ne akan su, kula da jin dadi da kuma nagartar rayuwar ‘ya’yansu. Hakan zai kai ga karesu daga fadawa hannun masu keta musu haddi a ko wane lokaci.”
Gwamnatin jihar Nasarawa ta kaddamar da shirin E-BAC tun a farkon shigowar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da nufin kawo karshen keta wa yara haddi.
Shirin gwamnatin Nasarawa na E-BAC wanda ke samun tallafi daga shirin inganta rayuwar yara ‘Sustainable Mechanism for Improbing Libelihoods and Households Empowerment (SMILE)’, shirin wanda kasar Amurka ke daukar nauyi da nufin gudanar da aiyukansa a cikin shekaru biyar masu zuwa.
Shirin SMILE wanda yake da nufin taimaka wa rayuwar marayu 600,000 da marasa galihu 150,000 da suke fadin kananan hukumomi 48 a da suke jihohin Benue, Kogi, Edo, da kuma babban birnin tarayya FCT tare da jihar Nasarawa, domin inganta wa yara rayuwarsu da kuma kare masu mutuncinsu da kimarsu daga masu neman salwantar masu
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!