Connect with us

TASKIRA

Illolin Da Zafin Rana Ke Haifarwa A Jikin Dan Adam

Published

on

Da yake Allah ya a jiye mu a tsakiyar duniya, kan wani guru da ya raba duniyar kashi biyu zuwa Arewa ko kuma Yamma, wanda masana taswirar duniya ke cewa ekuator, dole ne mu hasken rana zai fi shafa fiye da sauran kasashe da ke nahiyoyin Arewa ko Kudu. A irin wadannan kasashe namu da ke kan wannan guru, zafin yanayi kan kai maki 35 zuwa 45 a ma’aunin santigred. Idan aka hada kuma da zafin Hamada ta Sahara da ke busowa daga Arewa, wadda ta fara cin wasu sassa na arewacin kasar nan, abin ya kan iya wuce misali. Kasashen da suke sama ko kasan wannan guru na ekuator sun fi mu saukin jin zafin rana. A irin wadannan kasashe zafin rana baya wuce maki 30 zuwa 35 a ma’aunin na santigred. To a wadannan ’yan shekaru kuma sai masu binciken yanayi suka gano ma yanayin namu kara dumama yake. Suka kara da cewa yawan hayakin masana’antu da na ababen hawa a birane yana yin illa ga wani shamaki a sararin samaniya da ke kare mu daga illar zafin rana. Wannan shamaki da suka kira ozone layer yana karewa a hankali a hankali. Wasu daga cikinsu sun tabbatar da cewa rabon da a yi zafi irin na
wadannan shekaru a irin kasashenmu ya kai shekaru talatin. Su kuma kasashe masu sanyi, suna samun rikicewar yanayi, daga karuwar sanyi zuwa karuwar ruwan sama wanda kan haddasa ambaliya. A cewarsu, dumamar yanayi ce ke sa yanayin zafi yake ta karuwa a kasashe masu zafi kuma na sanyi yake ta karuwa a wurare masu sanyi. Yanayin zafi zai iya yin illa ga lafiya idan ya yi yawa, idan ba a dauki matakan kariya ba, kamar yadda yanayin sanyi sosai kan yi wa jiki illa idan ba a dauki matakan kariya ba. Zai iya kawo wata matsala a likitance ake kira heat stroke wato bugun rana. A wannan yanayi maimakon jiki ya yi zafi kamar na zazzabi, an fi samun kwakwalwa ce kawai take daukar zafi, idan abin ya yi mata yawa sai ta dan dakata da aiki, shi ya sa a kan samu suma, amma da jiki ya bar zafin sai ta dawo. Ya kamata kuma mu san cewa ba zafin rana ne kawai ke nan zai iya kawo wannan matsala ba, duk wani wuri da mutum zai shiga ya sha zafi abin zai iya karuwa. Misali, a kan samu haka a ma’aikatan gidan buredi saboda zafin wurin ko na kamfanoni wadanda injinansu kan yawan daukar zafi.
Alamomin da mutum zai ji a yanayi na zafi sun hada da:
1. Yawan bushewar baki da makogwaro.
2. Yawan zufa.
3. Fitowar kurajen gumi musamman a yara.
4. Dusashewar fata wato duhun fata.
5. Yawan ciwon kai.
6. Karancin fitsari ko kuma canjin kalar fitsari zuwa ruwan dorawa. Amma idan tsananin ya yi yawa, kwakwalwa ta kasa daukar zafin yanayin, a kan samu alamu na wannan tsanani kamar haka:
– Bayan ciwon kai sai a samu gigicewa.
– Ba za kuma a ga zufa ba, tunda rowan jiki ya kusa karewa.
– A wasu lokutan ana iya suma musamman ma a yara.
– Baki da Lebba za su yi fari fat.
– Jin muguwar kishirwa.

Hanyoyin kariya daga wannan yanayi.
* Yana da kyau mutum ya rika sa kaya marasa nauyi kuma masu haske ba masu
duhu ba, domin kaya masu haske suna rage yawan zafin da ke shiga jiki ta fatarmu, haka kuma kaya masu duhu su kan kara wa fatarmu jin zafin rana. Shi ya sa za a ga mutan da suna yawan sa ’yar shara fara a yanayi irin na zafi.
* A guji yawo ko motsa jiki cikin rana sai dai can da yamma ko da sassafe lokacin da babu zafin rana sosai.
* Idan ta kama sai an shiga rana yana da kyau mutum ya rike lema ko ya sa hula malafa wadda za ta yi masa inuwa. Mutane da yawa sun fi rike lema a yayin da ake ruwa saboda gudun bugun ruwa, amma da mutum ya san illar da zafin rana take ga jikinsa da zai rika amfani da lema a cikin rana ma.
*A rika ajiyewa ko tafiya da ruwa mai sanyi a kusa domin a rika sha a kai-a kai.
*Kamar kuma yadda wasu da yawa suke tambayar amfanin na’uraur sanyaya wuri,
to a irin wannan yanayi a gidajenmu da wuraren ayyukanmu wannan na’ura tana matukar taimakawa kwarai da gaske wajen sanyaya wuri da jiki ma baki daya.
*Idan babu irin wannan na’ura a kan samu fanka, wadda a yanzu a kan samu mai caji ko rike wuta a batir ko da ba a samun isasshiyar wutar lantarki.
* A guji fita da yara unguwa ko cefane a irin wannan yanayi. A kuma lura idan an fita da su, a daina barin su a mota idan za a fita, don kada zafin mota ya buge su. Ana yawan kawo irin wadannan yaran da aka bari cikin mota suka suma asibiti a lokutan zafi.
*Yana da kyau idan an shiga rana a yanayi mai zafi, da an dawo gida a watsa ruwa mai dan sanyi a jiki, don kwakwalwa ta huce.
* Idan mutum yana aiki a wuri mai zafi kamar gidan biredi ko kamfani inda injina ke zafi ko wadanda ke karkashin kasa wajen hakar ma’adinai, dole yan nemi yanayi da zai saukaka zafin kamar na’urar sanyaya wuri da maka-makan tagogi da sauran dabarun sanyaya wurin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!