Marasa Kishi Ke Neman Takara Da Buhari A 2019 –Dakta Alyusra — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

SIYASA

Marasa Kishi Ke Neman Takara Da Buhari A 2019 –Dakta Alyusra

Published

on


Yanayin siyasar Nijeriya na ci gaba da sauyawa saboda kurar da ke tirnike yanayin musamman daga lokacin da batun ‘R-APC’ da kuma hadin gwiwar jam’iyyun adawa suka ce za su yi wajen fitar da dan takara daya tilo da zai gwabza da Shugaba Buhari a zaben 2019. Malami kuma mai fashin bakin al’amuran yau da kullum, Dakta Jamil Nasir Bebeji ya ce wa duk masu neman takara su hakura har sai Shugaba Buhari ya kammala shekara takwas a gadon mulkin kafin su leko kai. Ko me ya sa? A karanta hirar da ya yi da wakilinmu a Abuja.
Da wa muke tare?
A’uzu billahi minasshaidanirrajim, Bismillahirrahmanirrahim, wassalatu wassalamu ala Rasulullah wa’ala alihi wasahabihi, waman walah.
Sunana Jamilu Nasir Alyusra.

Kana daga cikin Malam addinin Musulunci, wane tsokaci za ka yi game da abubuwan da ke gudana a kasar nan?
A yanzu dai abin da yake damun kowa a wannan kasa shi ne, maganar siyasa da ake yi, mummunar siyasa da ake gudanar da ita a Nijeriya, abinda ya san a kira ta da suna mummunar siyasa, saboda duk yadda kake son mulki, to ka fara duba maslaha wato abin amfani ga jama’arka inda kake so ka mulka ba kai abin da za ka samu ba.
Siyasa a Nijeriya an dade ana yenta, wannan Shugaba ya hau, amma Allah bai taba ba mu Shugaban da ni naga cewa yana so ya yi gyara kamar Shugaba Muhammadu Buhari ba.
Kuma kowanne mutum Musulmi da wanda ba Musulmi ba, da kowanne yare ya tabbatar cewa Muhammadu Buhari shi ba barawo ba ne ba ya sata, a wannan dalili nake ganin cewa duk mutum mai hankali abin da makiyansa suke kawowa, sai su rika cewa, ai shi baya yi amma na karkashinsa su ne ba mutanen kiriki ba. Abin da farko azzalumi in yana so ya ruguje wani, to na ginsa yake fara rugujewa, don ya san shi babban ba zai tabu ba.
Misali wasu daga cikin masu akidu marasa kyau idan suna so su zagi Manzon Allah, sun san in suka zage shi mutane ba za su yarda ba, sai su rika sukan Sahabbansa. Ta ka ga ai shi suke so su ruguje. Amma ba zai ruguzu ba, saboda ayyukan da yake yi a fili da suka gagara wadanda ya yi a baya gasu a fili suna gani.
Idan a siyasance idan mutum zai kallain har yana son al’ummarsa, to ni sai in ga kamar cewa, ko wane dan neman takara ya sallmawa Buhari, ba ruwana da APC ko PDP, a’a ina kallon halin da Nijeriyar kanta take ciki, ka duba daga matsalar wutar lantarki, da matsalar rashin tsaro, da matsalar talauci, da hauhawar farashin kaya wadannan matsalolin tun-tuni akwai shi. To wanene a zahiri ya fito ya nuna zai yi gyaran?Sai Muhammadu Buhari din.

Akwai talakawan da ke cewa Shugaba Buhari ya gaza yi musu abin da suke bukata kuma gashi mulkin kusan yana shirin karewa, ta yaya za ka fitar da shi daga wannan zargi?
Misali kamar me?
Akwai wadan da suke cewa da zarar ya hau mulki kakarsu ta yanke saka, sai kuma a cewarsu ya zama sun samu kuncin rayuwa…
Ai duk wani masani mai hangen nesa ya san ba yadda za a yi a a yi gyara cikin jin dadi, ko ka yi ba ka isa ka ce an gyara ka ba tare da ka ji zafi ba, ba zai yiwu ba. Dole barnar da aka yi Nijeriya in aka zo gyara ta sai an shiga cikin kunci, domin sai an tare wasu abubuwa an hana wasu abubuwa, sannan wasu abubuwa za su tabbata.

Malam wadanne abubuwa za ka haskawa jama’a narawar ganin da wannan gwanati ta yi da za a samu kwarin gwiwar sake zabenta a nan gaba?
To na farko idan muka kalli matsalar tsaro da ake da ita a Nijeriya gaba daya, to Buhari ya yi rawar gani waje kashi 60, ya taka rawa a matsalar Biafara, yanzu maganar Biafara babu ita, yayi maganin matsalar Boko Haram, duniya gaba daya sun sara masa, yana kan maganin matsalar satar shanu da ake yi a wasu garuruwa, wanda kowa ya sani za a zo gari tun shekaru da dama, a zo har da jirgi ma ake zuwa a kwashe shanun mutane, a kashe gari guda na Fulani a kwashe masu dabbobi.
Amma daga hawansa aaka rika har har Bariki guda na soja ya kafa a jihar Zamfara saboda a yi magani satar shanun.
Jin haushin an hana su satar shanun ne, sai su bullo don suna jin yunwa, sai su zo su yi wa mutum fashi a garuruwa irinsu Zamfara din dai, su kashe mutane a banza su kwashi abinci su wuce. To ka ga Buhari da ya hau ya yi ta kokarin wannan, sannan in ka dubi hanyoyin nan, hanyar Legas ya gyara ta, hanyoyin da suka hada da garin Inyamurai duk yayi su, garinsu Jonathan ma na gani a labarai ban je ba, amma in ta tabbata haka ne, gasu nan suna murna cewa dansu ya hau bai yi masu, amma kuma ga Buhari nan ya hauyayi.
Hanyar Kano gashi nan a ba wa ‘Julius Berger’ da suna ta kukan ba a yi masu ba, ga shi yanzu a shekaru ‘yan kadan gashi yanzu hanya wadda ta taso tun daga Kano har zuwa Abuja. Wutar lantarki ko makaho ya shafa ya san cewa an samu ci gaba ninkin -ba-ninkin akan yadda ake a baya, sannan bangaren da ya shafi harkar lafiya, ita ma kanta kowa ya sa cewa a yanzu a asibitoci ana samar da kayan zamani, domin gashi nan ana bubbudewa, kowane gwamna yana nan yana kokari a karkashin wannan mulki na Buhari ya samar da kayan zamani a asibitocinsa.
To wadannan abubuwa in suka gyaru aka sami wutar lantarki, aka samu tsaro, aka samu hanyar da sada mutune, to ka huldar kasuwanci zai tafi yadda ake so. To kuma ga hanyar da sadar da mutane cikin sauki, ita ce hanyar jirgin kasan nan, ita ma gata ana kokarin za a yi ratsa ko ina cikin kasar nan, kuma hanyar zamani. Kuma ga wadda za ta sada kasa da kasa, yanzu ga shi ana maganar a Disambar nan idan Allah ya tabbatar za a dawo da kamfanin jiragen sama na Nijeriya wato Nigeria Air Ways’ ya fara zirga-zirga kamar yadda muke ganin na wasu kasashe na yi.
Wannan ba abin kunya ba ne a ce Shugabanni sun yi mulki sun yi mulki, kuma suna da jiragen kansu na hawa? Pasto a garin nan za ka samu yana da jirgin kansa na hawa amma a ce Nijeriya ba ta da jirgin kanta wanda dan Nijeriya zai hau yayi farin cikin ya hau jirgin kasarsa kamar sauran ‘yan kasashe.?
To duk Shugabannin sun kasa yi, amma yanzu Buhari ya zo zai yi shi, in suka tabbata Allah ya sa suna tafiya, to ai kuma babu abin da zai rage sai kirkrar yadda za a yi kudi su tabbata a hannun mutane, daga kuma sai ka ga darajar naira ta dawo, tunda wutar lantarki ta samu hanyoyi sun samu, ga tsaro ya tabbata, masana’antu sun mike. To ‘yan waje za su yi ta ruguntsumowa,kuma hakan ne zai sa ka ga ita kanta dalar ta kara sauka fiye da yadda ake tsammani, daga nan kuma kudin Nijeriya zai kara daraja. To ka ga sana’o’i za su yi yawa kowa zai kasance cikin wadata.

Mu koma baya kadan ka maganar kashe-kashe, kana wata shawara da za ka ba wa gwanati a kan yadda za ta shawo kan matsalar?
Eh, shawarar da zan bayar ita ce, Buhari ya daina yin sanyin jiki, yana da sanyin jiki da yawa saboda shekaru da suka same shi. Dole ne a muliki wata ran sai an ciza sannan a busa, ya daure ya daina ganin girman duk wani mai girma da zai kawo matsala ga al’umma, ya bibiyi asali ya gano su waye suka daure musu gindi, tabbas duk wani fasadi babba da kake gani akwai hannun wasu manya a cikisa, ya matsa wajen kama wanda suke da hannu a cikinsu ko su waye ko waye ya daure masu gindi a duniya kuma a hukunta su, amma matukar za a yi ta rurrufawa karfinsu zai cigaba da bunkasa, za su ci gaba da yin abin da suke so, domin su suke dasa su kuma suke tunzura su domin cimma wasu manufofi na siyasa

Ba ka ganin maganar gyara hanyar jirgin kasa da kuma dawo da ‘Nigeria Air ways’ ba ka ganin wasu za su ce an yi ko yi ne da gwamnatin da ta gabata?
To ai yin hakan ba laifi ba ne, in yayi koyi da gwamnatin da ta gabata, ai idan mutum azzalumi ne in ya zo sai ya ce sai ya rushe duk abin da gwamnatin baya ta yi. Amma mutum mai adalci shi ne wanda in ya zo ya ga wani tsari da gwamnatin baya ta doro mai kyau sai ya dora a kai ya mike.
Misali ai abubuwan da gwamnatin bayan suka dinga fada a jaridu, da labarai, ka rika murna kamar an gama aiki, sai ka ga har an kaddamar, amma ba za ka ga komai ba, gashi dai tsarin mai kyau ne in ka gani amma iyakacinsa baki. To shi kuma Buhari yana shi ne a tabbace, misali abin da mu dai muka fahimta, da ya zo ya karanta ya duba ya ga cewa tsarin ai mai kyau ne, saboda haka kawai sai yake yinsa a aikace, na su bai da amfani domin sun shi ne bisa yaudara, to ko sayarwar da suka ce sun yi da suka sayar din ina kudin suke? Suna aljihunsu.

Nigeria Air ways da aka sayar ina jiragen? Duk abin da suka ce sun sayar ina kudi?
Sayarwar da suka yi ba ta amfanar ba, domin wasu na zargin ma su suka sayar wa da kansu. Kuma da aka sayar ai da muga kamfanonin sun zo da kayan aiki suna ta amfani da su mu ma sai mu ji dadi, amma babu ko daya. An sayar da wutar lantarki ana karbar kudin wuta, amma ba mu kamfanin ya zo yana ta gyare-gyare ba, sai ku yi wata daya ba ku da wuta, idan ma an kawo ta ba za ta fi awa daya ko biyu ba, sai a dauke. Kuma da ya zo ya tarar duk an sayar sai ya gat sari ne mai kyau don haka ya dora a kai, don haka ba laifi ba ne don ka samu wani tsari mai kyau daga gwamnatin da ga inda aka dora a inda ta tsaya, hakan ma shi ne adalci.

Wane abu da wasu daga bangaren Arewa suke zargi shi ne, gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta fi fifita yankin Kudu fiye da Arewa wajensamar da ayyukan cigaba, a mahangarka yaya abin yake?
Wannan bah aka ba ne, akwai rabe-raben ayyuka a shugabanci, idan kana Shugaba na gaba dayan wannan kasa, to bai kamata ka nuna bangarenci ba. Buhari da ya hau mulki, ya samu akwai Hausawa, akwai garin Yarbawa, akwai kuma garin Inyamurai. Dolensa ne ya nutsu ya ga ko wanne bangare mai ya fi a lokacin, sai yayi masa abin da ya fi so, gaba daya maganar tsaro magana ce da duka Nijeriya, amma Arewa tana da wata matsalar tsaron ta musamman mai girman gaske, ita ce matsalar Boko Haram din nan, to saboda haka abinda Arewa suka fi so shi ne a kau da Boko Haram, don haka kudade ake narkawa na fitar hankali wand aba zan iya fadar alkalumansu yanzu a bakina ba, amma kudade ne masu ciwo.
Bayan aikin samar da tsaron da yake yi, sai kuma ya zo yana yin ayyukan hanyoyin nan, saboda Allah wannan bai zama adalci ba.
To da ya juya daya bangaren sai ya ga ba su da ruwa, ba su da hanya, su kuma ya dauki kudi ko da bai kai wannan tsaron ba in ya je ya yi masu. Domin ina tabbatar maka da cewa kudin da aka kashe a harkar Boko Haram dinnan, ba a kashe rabinsa agarin Yarbawa da Inyamurai ba a iya shekarun nan da ya yi.
To sannan Legas ma suna bukatar hanya ta jirgin kasa da sauransu, ya je yake yi masu, sannan yake kokarin tayar da masa’antar Ajaokuta din nan. Da ya ga ya ci karfin matsalar tsaro a Arewa, ba sai ya bullo da maganar gyaran hanya har yake maganar gyaran wutar Mombila ba, kuma yake kokarin hade hanyar da za ta hade ka da jihar Filato? Duk wannan abubuwa ne muhimmai, kuma yake kokarin yashe kogin Neja ko? Kogin da ake cewa jirgin ruwa zai rika zuwa har Neja yana sauke kaya, wanda dama yana cikin tsarinsa tun sanda yana Kamfen, amma bai iya aiwatar da aikin ba, saboda kudin yana ta mafani da wajen harkar tsaro.
Yanzu da ya cewa yah au sai yake yi, kuma a yanzu ma aikin da yake wa Arewa yana so ne ya ga ya mata da man fetur, kuma kudi yake narkawa. To kuma kudin da ake narkawa ba lallai ne a gansu a zahiri ba, domin ba kamar titi da ake shimfidawa ne ko wasu abubuwa iran wadannan, ba abu ne da za a gansu a zahiri ba, abu ne mai muhimmanci da ya fi titin ma ta wani gefen, ama kuma ba za a ganshi a zahiri ba.
Saboda babu maganar wani nuna son Arewa, ba haka bane, sanda Buhari bai hau mulki ba a Kudu yake ko a Arewa, in ya sauka daga mulki a ina zai zauna? A Arewa yake kuma a Arewar nan zai zauna, amma ace da inda yake da kuma inda ba a nan yake ba, a ce wai ba ya son inda yake, wannan ba gaskiya ba ne.

To a kwanan nan akwai jam’iyyun taron dangi da suke son sai sun kayar da Buhari a zabe mai zuwa, yaya kake ganin tasirin abin a siyasar Shugaba Buhari?
Ita ce maganar da fara yi tun farko, cewa duk wani dan takara musamman na Shugaban kasa, in dai har ya tsaya neman takarar Shugaban kasa, to ina tabbatar maka da cewa makiyin talakawa ne, kuma ba adali bane.saboda Nijeriya ce ta lalace, lalacewar da a yanzu ba zai yiwu na yi maka bayani filla-filla ba. Misali PDP da muke so gaba daya Nijeriya shekaru 16 din nan da ake ta magana, ta yi mulki iya mulki, amma gaba daya ta lalata komai, ta kwashe kudi gashi asiri yana ta tonuwa. Kuma su wadannan mutanen da muke fada cikinsu wasu sun yi gwamnoni, kuma da su aka yi waccan gwamnatin da aka yi wannan ta’asarsun kasa tabuka komai, to a can ya kamata mu ga irin gudunmawar da za su bayar wajen gina kasar.
Sai da suga Buhari zai ci mulkinwai gasusun dawo wai ‘yan APC, munafukai ne, aunawa suka yi suka ga a wannan lokacin in ba wurinsa suka koma ba, ba za su ci zabe ba.Suka ci zaben don su tabbatar munfarsu ba don su tabbatar manufar Buhari ba, shi ya sa yanzun ma Alah ya tona asirinsu.

Akaramakallah wasu za su ceai kundin tsarin mulkin kasa ya ba wa ko wane dan Nijeria dama in har ya isa tsayawa takarar Shugaban kasa ya tsaya, ba ka ganin suna ‘yancin su nemi takara?
Ai dama da ‘yancin ne nake magana, ‘yan kai kana yi ne don kanka ko kana yi ne don mutune? Tun da dai kana yi ne don mutane, duk kaninsu sun kai shekara 60, tun suna shekara 30 da kaza suke mulkin Nijeriya, me ya sa ba su yi gyaran ba. Akwai wanda yayi gwamna a cikinsu bai gyara jiharsa ba, wani yayi minister bai yi wani abin kirki ba, wasu suna kan sanatoci kuma babu abinda suka yi, kuma duk wani ha’inci da cin amanar kasa da su aka yi.
Menene ya sa ga wanda ya zo a zahiri ya zo yana yin wani abu da ya gagara, ga masa’antu yana ta tayarwa wadan da ada sun mutu, yana ta dawo da darajar Nijeriya, kuma mutumin nan ya tsufa in ba zalama ba, ku bar shi cikin abubuwa biyu daya zai faru ga Buhari, ko da Allah yayi mashi rasuwa, ko kuma dolen shi ya sauka, domin daga takwas dinnan Buhari in ba a keken guragu za a rika tura shi ba, shekarunsa sun kai shi ma hakura zai ya ba wa wani.
Abin da nake nufi misali, da cikinsu ba a taba samun wanda ya mulki Nijeriya ba, ma’ana bai taba rike Minista ba, bai taba rike gwamna ko dan majalisa ba, ya fito ya ce na ga gazawar Buhari, to sai mu ce watakila gara shi, ba za mu zarge shi ba tun da bai yi mun gani ba. Amma fa kaga har akwai wanda ya taba rike mukamin mataimakin Shugaban kasa acikinsu.
Na gaya maka inda nake ganin laifin Buhari kawai yadda yake tausawa wadan da suke da hannu akan shiryawa kasar nan makarkashiya, da kuma yi masu kawaici, don wannan kawaicin illa ce babba. Dole idan mutum azzalumi ne kamo shi in na daurewa ne ka daure shi, in na harbewa ne ka harbe shi, in na yankawa ne ka yanka shi.

Akaramakallahu wace magana ce ta karshe da za ka fada?
Maganar dai ita ce, su talakawa kada su zama wawaye akan dan abin da za a ba su su zubar da mutuncinsu na dindindin, ya kamata su marawa Buhari baya, saboda Malamanmu sun yi mana wasici da haka, kuma muma muna wasici da hakan. Shi kadai ne da a yanzu muke sa rai da fata akan cewa zai gyara Nijeriya, ta ko wace fuska in dai aka cigaba da mara masa baya. Kuma wadannan da suka fito suke neman su yi takara da shi a yanzu, kamata ya yi in dai wani ya taba rike wani mukami sau daya to kada a zabe shi. Domin an ga abin da suka yi a baya ba su yi abin da Buhari ya yi a yanzu ba, tun da ba wasu sababbi ba ne, don haka talaka ya zama a cikin hankalinsa yayi wa kansa gata, domin Buhari ba yana yi wa kansa bane, kawai wahala yake yi wa talakawa. Saboda haka idan ka yi zabe Buhari ya fadi kai ne ka cuci kanka, wannan ita ce shawarar da zan ba wa talakawa in sha Allahu, salamu alaiku.

Advertisement
Click to comment

labarai