Muhimmancin Neman Ilimin Aure Kafin A Yi — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

Madubin Rayuwa

Muhimmancin Neman Ilimin Aure Kafin A Yi

Published

on


Babu shakka mun shiga zamani (lokaci) wanda matasa maza da mata ana yin aure ne ba tare da muna da ilimin auren a addinan ce ba.
Mu dai kawai mun tashi muntaras da iyayenmu sun yi aure, yayunmu sun yi aure , abokanmu suma suna ta aure, don haka muma yakamata mu yi auren nan kar abarmu a baya.
Haka za ka ji matasa suna ta fadi, saboda an dauki aure kamar wani al’ada ce ta mutane kuma abin a more a ji dadi.

Hakan ya sa dayawan mutane wanda suka yi aure ba tare da ilimin yadda za su tsarkake niyyansu game da aure ba, wanda hakan ya sa bayan sun yi auren sai suka tarar da rayuwan babu dadin da suke tsammani, sai ka ga suna cewa ai aure zaman hakuri ne kawai a cikin sa, babu shakka aure zaman hakuri ne ko ka fada ko baka fada ba wannan sananne ne a gun wanda ya san hikimar aure a addinan ce.

Yanzu halin da ake ciki matasa mun koma auren ‘yan mata ne saboda kyawun surarsu ko kuma kyawun baiwan da Allah ya yi musu, wanda hakan yana daya daga cikin auren sha’awa kamar yadda malamai suka yi bayani. Matasa na auren mace ne irin wanda idan suka nunata a dangi za a ce dasu kai gaskiya matar wane ta hadu, ai wane ya iya zabe da sauran su. Saboda ya bi kyawun surar jikinta ko fuskarta wanda wannan abu ne mai gushewa cikin kankanin lokaci.

Dayawan maza idan suka auri mace don kyawun suranta, ko kyawun fuskarta za ka taras bayan an yi auren zai dawo daga baya zai zo baya ganin wannan kyawun nata sosai, saboda yau da gobe kullum yana ganin fuskar harma zai zo ya zamana kyawun baya masa tasiri, sannan maza mun kasance muna fita waje dole za ka ga wanda tafi matarka kyawun sura ko fuska. Idan dama abin da yake birge ka kenan to sai ka ga fa kai yanzu ita wannan na wajen itane ta fi birge ka saboda ta fi naka na gida, sai ka ga mutum ya fara nemen mata, shi ya sa wannan yana daya daga cikin manyan dalilin da suke sa maza su rika canzawa matansu bayan an yi aure .

Za ka ga na miji rimi-rimi a waje kafin aure sai ka ga yana lallamin ta kamar me, amma daga zaran ta shigo cikin gidan sa zai fara canza mata ahankali-ahankali, saboda ya sami abin da yake bukata, don haka ko a yanzu kasuwa ta watse dan koli ya ci riba, sai ka ga yana kuntata mata iri-iri na yau daban gobe daban, Me ya sa haka? Saboda ba don Allah ya aure ta ba, ya bi zabin san ransa ne amma bai dauki auren a matsayin ibada ba.

Duk wanda ya dauki aure a matsayin ibada kamar yadda ya dauki sallah da azumi ibada to babu shakka za ka ga ya kyautata niyyarsa sannan za ka taras da shi yana kokarin kyautata wa matarsa.

Amma duk wanda ya yi aure don sha’awa saboda a ji dadi a huta, to babu shakka za ka taras da shi daga baya zai zo yana wulakanta matarsa saboda bukatarsa ta biya, yanzu kuma ta zama masa kamar nauyi ne, sai ka ga yana canza mata halayensa kamar yadda hawainiya take canza kalar fatar jikinta idan ta so a kuma lokacin da ta so.
Ya Allah ka tsare mu da auren sha’awa bisa jahiltan hikimar aure a muslunci, ya Allah ka gyara mana zukatanmu ka ba mu ikon kyautata niyyanmu.

Advertisement
Click to comment

labarai