Nadal Da Djokobic Za Su Fafata A Wasan Wimbledon A London — Leadership Hausa Newspapers
Connect with us

WASANNI

Nadal Da Djokobic Za Su Fafata A Wasan Wimbledon A London

Published

on


Gwarzon dan wasan Tennis lamba daya na duniya Rafeal Nadal dan kasar Sipaniya zai fafata da abokin hamayyarsa Nobak Djokobic na kasar Serbia, a zagayen kusa da na karshe na gasar Wimbledon da ke gudana a London.
Karo na shida kenan da Nadal ya samu kai wa zagayen kusa da na karshen a gasar tennis ta Wimbledon, bayan da a wasan kwata Final na ranar Laraba, Nadal din ya samu nasara kan Juan Martin Del Potro na Argentina da kwallaye 7-5, 6-7, 4-6, 6-4 da kuma 6-4.
Sai da aka shafe sa’o’i 4 Nadal da Del Potro suna fafatawa kafin Nadal ya samu nasarar da kyar wadda tabashi damar zuwa wasan na karshe.
Sau 51 aka taba haduwa a wasan na tennis tsakanin Djokobic da Nadal, inda Nadal ya samu nasara sau 25, Djokobic kuma ya samu nasara akan Nadal sau 26.

Advertisement
Click to comment

labarai