Connect with us

Madubin Rayuwa

Sakacin Iyaye Ke Sa Dalibi Lalacewa A Jami’a – Sadik Ahmad

Published

on

Kamar dai yadda wannan shafi ya saba zakulo muku mutane daban-daban daga bangaren maza da kuma mata na cikin manyan Makarantun gaba da sakandare dan jin ta bakinsu. A yau ma wannan shafi ya tattauna da daya daga cikin daliban da suka sha fama kan neman ilimi.
Ga kuma yadda hirar ta kasance:

Ya sunan Malamin?
Sunana Sadik Uba Ahmad

Masu karatu za su so su ji dan takaitaccen tarihinka?
An haife ni a karamar hukumar Bunkure dake Kano state nayi primary school dina da junior school (2005-2008) dina a Bunkure daga nan na zana jarabawar science and technical nayi nasara naci na tafi Dawakin Tofa Science College (2008-11) dake karamar hukumar dawakin tofa. Bayan na gama na dawo nayi CAS (2011-2013). Daga nan na dawo Bayero Unibersity Kano (2013-17) inda na yi ‘degree’ dina na farko a bangaren Technology (Fasaha) karkashin Electrical/Electronic (Kimiyyar lantarki).

Idan muka koma kan abin da ya shafi karatunka, shin Kafin ka kammala Makarantar Sakandare wacce makaranta ka yi burin shiga?
Kafin na kammala secondary school ina da burin zuwa Maiduguri Federal Unibersity dinsu sai kuma aka fara rigimar Boko Haram sai nayi tunanin in tafi jami’ar Ahmedu Bello dake Zaria (Abu). Amma Allah bai yi ba, muna gama CAS da nayi IJMB (Jarabawar share fagen shiga jami’a) na cike DE sai na Nemi BUK da KUST da ke Wudil. Na yi dace KUST suka bani Lebel 2 BUK lebel1 Amma Allah da ikonsa sai baban mu ya ce yafi san BUK haka na hakura naje na yi.

Da kyau! Kafin ka shiga Makarantar jami’a wacce irin gwagwarmaya ka sha wajen neman samun ‘Admission’?
Eh! gaskiya na sha gwagwarmaya sakamakon abunda na nema bashi aka bani ba, na nemi Cibil Engineering aka bani Technology Electrical/Electronic. Karatun ya bani wahala sakamakon ban taba yin courses din Education ba sai da na fara Technology dina.Tun bana ganewa ina hakuri har nazo ina fuskanta ya zamto ma nine nake koya wa wasu.

Ko zaka iya tuna sabbin abubuwan da ka fara cin karo da su tun daga kokarin da kai wajen cike form da rajistar babbar makarantar?
E, a lokacin da na yi karo da JAMB dan ta yi matukar bani tsoro tun da ban taba yinta ba sai a shekarata ta karshe a CAS. Allah kuma ya taimaken na samu 246. Sannan na dawo da hankalina kan ijmb dan ita kuma tafi jamb kalubale da wahala itama Allah yasa na samu 10points. Hakan yasa jami’ah ta zamo mai saukin samu a gareni ta hanyoyi biyu.

Ya batun wajen zirga-zirga na cike-ciken takardu da sauransu kafin shigarka jami’ar ya ya kasance?
Dake komai Ya koma na yanar gizo-gizo ban sha wani wahala ba gaskiya.

Gaskiya ne! Bayan ka shiga jami’a ko zaka iya tuna mutanen daka fara cin karo da su?
Gaskiya dana shiga dake a bangare ban san kowa ba haka naita yawo na har nazo na zama dan gari. Nayi abokai dan saida ya zamto kusan kowa ya sanni a ajinmu.

Toh! Yaya farkon shigarka aji ya kasance?
To dake a baya na saba da gwagwarmaya a CAS ban ji komai ba kawai dai na jini babu sukuni tunda nazo tunda ban san kowa ba.

Ko zaka iya tuna sunan wanda ka fara zama kusa da shi/ita farkon shigarka aji?
Mace ce sunanta maryam, Kuma itace wacce na fara haduwa da ita dan itama ranar dana fara zuwa taje.

In na fahimce ka rana daya kuka je da ita, Toh! Ya darasin ranar ya kasance?
Eh! Rana daya muka je, Dake a ranar Sociology ne, ji nayi wallahi tankar na koma gida nace bazan karatunba dan ban taba tunanin Sociology course ne ba.

Lallai! Toh! Me ya sa kaji hakan?
Sakamakon ban taba yinsa ba a ‘secondary school’ dina ba

Shin ya baka wuya ne a lokacin Ko kuwa dai ya abun yake?
Gaskiya ya bani wuya sosai.

Bayan da ka shiga ajin ka zauna ake muku darasi ya ka kasance har zuwa lokacin da aka tashi?
Kawai guri na samu na zauna ina sauraran darasin amma fa bana ganewa dan a karshema malamin ji nayi ina jin haushinsa. Ikon Allah a gefena akwai wani abokina alokacin ban san shiba sunansa Abdulkadir ddn katsina ne nake tambayarsa “waiko kana fuskanta” yace “babu abun da yake ganewa”. Da nake tambayarsa sai na fuskanci shima irin matsalatace da shi.

Da su wa ka fara abota a farkon zuwanka kuma mene ne musabbabin zamanku abokai ?
Na fara abota da ‘yan ajin mu irinsu Mahmud, Abdullahi, Naziru, nafi’u da sauransu, ya zamto bani da wadanda muke yawo ko zuwa cin abunci sai da su.

Sai dai ba ka fadawa masu kararu Musabbabin haduwarku ba, mece ce silar haduwarka da abokanka?
Karatu kuma na gansu nutsats-tsu sun san abunda ya kawosu sun san ciwon kansu.

Da Kyau! Ya zirga-zirgar zuwa makarantar ka ya kasance ?
Na yi zaman hostel a old side duk da yake duk lectures dina a new side nake yi to sakamakon ina da lifan dina da shi nake amfani har na gama degree dina ban taba kwana a new side din ba.

Me ya fara baka tsoro ga makarantar jami’a?
Ya nayin jarabawarsu dan gaskiya tana da tsauri gashi da ka sami matsala sai ta zama carry ober idan kuma makinka ma bai kaiba a koreka daga makarantar gaba daya. Dan ba zan Mantaba ina farkon zuwana naje na duba board naga an kori mutane hankalina yai matukar tashi dan sai da na yi tunanin nima haka zai iya kasancewa a kaina.

Ya zamantakewar rayuwar jami’a take, kamar yanayin irin shigarsu da kuma mu’amular maza da mata na makarantar?
Eh to gaskiya yana yin rayuwar Jami’ah ba ruwan wani da wani sai dai kowa harkokinsa yake yi maza da mata. Tsarin shiga kuwa makaranta ta ware irin shigar da ake bukatar kowa ya yi wacce ta dace da a yi a darsu da ke akwai kabilu kala-kala. Da shiga bakin gate akwai hoton Allo da aka kafe ke dauke da tsarin kayan da ake san kowa Yayi koyi da irinsu ya danganta da yarenka.

Toh! Ya batun da a ake cewa wasu in suka shiga jami’a dabi’unsu sukan canja su koma irin dabi’ar da ba tasu ba haka kuma wajen shigar kaya (dressing) wasu sukan baro gidansu da shigar kamala amma da zarar sun bar gida sai su nemi su canja shigarsu su shiga makaranta a haka, shin ya abun yake?
Eh maganar gaskiya hakan tana faruwa sosai a farko zaki ga saurayi ko budurwa da kamalar su da dabi’u masu kyau da shiga ta musulunci amma daga baya su canza kuma hakan yana samo asaline daga abokai ko kawayen daba nagari ba. Yarinya sai ta baro gida da katon hijabi da kaya na kirki amma tana zuwa Jami’a kawai sai ta rinjayeta ta canza mata alkibla. Wallahi idan wani ko wata suka yi wata shigar sai mutum ya rantse ba musulmai ba ne, Kuma gaskiya makaranta da malamai suna yin iyaka kokarinsu amma da ke an ce danbu in yayi yawa ba ya jin mai sai a ga ba sa magana.

Hakane! Ko ka taba cin karo da irin wa ‘yan nan abokan?
Eh! to gaskiya da ke hausawa na cewa idan kana san ka san halin mutum duba halin abokansa, hakan ya sa ba na saurararsu ko kula su bare ma hakan ta kasance a kaina su canzamin tarbiyata.

Ya kake ji a zuciyarka a duk sanda kaci karo da masu irin wannan halin?
Ina yi musu addu’ah da Allah yasa su gane dai-dai. Kuma nakan ga sakacin wasu iyayen da basa bibiyar yaransu a manyan makarantu.

Wacce shawara za ka bawa masu irin wannan hali?
Su ji tsoran Allah su tuba dan basu dauki hanya mai dorewa ba.

Wanne darasi ne ya fi ba ka wuya, kuma me ya sa?
Education (Malanta), Sakamakon ban taba yinsa ba a sakandare dina.

Wanne darasi ka fiso? Kuma me ya sa kake son sa?
Darasin Math (Lissafi), sakamakon na fi gane shi kuma babu wata hadda in ka iya ka iya, Amma bani da matsalar courses din electrical musammanma mathematics dan ina matukar san lissafi.

Wacce daliba ce tafi burgeka a ajin?
Hmm gaskiya ba zan iya fadin sunan ta ba sakamakon da matsala amma kuma na san ita da ta gani za ta san da ita nake.

A maza fa waya fi burgeka?
Mahmud Adam kankarofi

Wanne malami ne yafi burgeka,Me yasa kuma yake burgeka?
Malan Abba Ibrahim, Ba shi da jiji da kai ga iya mu’amala ga dalibai ga san taimakawa duk wani dalibi kuma bawai ni kadai yake burgewa ba duk dalibanne.

Mene burinka kafin ka kammala Makarantar jami’a?
Babban burina in ga na taimaki na asa dani sannan inna kammala karatuna na zamo lecturer dan ina buatar taimakawa ‘yan uwana musulmai.

Da kyau! Mu koma ga wata tambayar ta gaba, Idan mace tana ci gaba da makarantar gaba da sakandare ko ta kamallah za kaji samari na cewa ba zasu aureta ba gwara sunje sun samo wadda bata karasa gaba da sakandare ba shin mene naka ra’ayin game da irin yarinyar da zaka aura?
Hmm hakane tabbas maza suna cewa ba zasu auri macen Jami ah ba. Kuma nima ada ina da wannan ra ayin sakamakon ganin canjin ra’ayi da dabi’u da suke canzawa. Bayan na shiga Jami’ah na gane cewa ba dukane suke da wannan dabi’arba. Ayandu hakama ni wacce nake burin Aura sai wacce tayi makarantar gaba da secondary.

Mene ra’yinka game da cigaban karatun mata a jami’a?
Ina goyon baya dari bisa dari dasu cigaba dakaratunsu ajami’ah, Kawai dai iyaye da mahukunta su saka idanuwa akan su.

Ya zaka banbantawa masu karatu banbancin macen da tayi makarantar gaba da Makarantar sakandare da kuma wadda bata yi ba?
Ai kaman ceceniyar ma bata kadanba dan ko iya wayewarma da iya zama da mutane da sanin kunci da dadin rayuwa wannan duk sai macen da tayi makarantar gaba da sakandare.

A naka hangen Wanne amfani karatun mace yake da shi ga al’umma?
Ai yana da matukar amfani tunda annabin mu ma yace duk Wanda ya baiwa mace ilimi tamkar ya bawa Al umma ilimine.

Da kyau! Ya batun Soyayya fa, Shin ko ka taba yi sanda kana jami’a?
Eh

Ya soyayyar ta kasance?
Soyaiya maitsafta mukayi tana sona inasanta

Shin har yanzu kuna tare?
Yanzu bama tare sakamakon wani dalili mai karfi.

A gurguje ko zaka bawa masu karatu labarin yanda ka kammala karatunka a jami’ar tun daga farkon farawarka har karshe?
Alhamdulillah na gama karatuna ba tare da wata matsalaba tun farkon shigata harna kammala kuma alhamdulillah na samu sakamako mai kyau dan na fita da second class upper. Shiyasa nake bawa ‘yan uwana dalibai shawara da komai za suyi Su sanya Allah a farko sannan a dage da karatu da addu ah insha Allah baza aji kunyaba

Da kyau! Wacce shawara zaka bawa masu kokarin shiga makarantar jami’a?
Su sa a ransu za su yi karatu dan Allah ba wai dan su tara abun duniyaba. Kuma su kula da addininsu da al adarsu Susan duk abun da kake yi Allah yana kallonka Ayi kuma karatu sosai sannan ayi addu ah. Dan daya baya yiwuwa ba tare da daya ba

Ko kana da wa ‘yanda zaka gaisar?
Eh, Ina gaida iyayena da duk malamai na tun daga kan primary Teachers dina har zuwa na Jami’ah. Sai kuma abokaina suma duk da babu lokacin lissafasu amma zan anbato kadan daga ciki Mahmud Adam kankarofi, Maryam Musa, Abdullahi alhassan Yusuf, muhd uba tijjani, Aisha Mustafa, Anisa aliyu, Hassan sani, Suleiman Adam,Aisha idris, maryam sinusi, Da duk ragowar ‘yan uwana da abokan arziki dan babu lokacin lissafasu.

Gaskiya ne, me zaka ce da masu karatun jaridar leadership da kuma shi wannan shafin na duniyar makarantu?
Ina yiwa jaridar LEADERSHIP A YAU JUMA’A fatan alkhairi Allah ya kara daukakata. Shi ma shafin duniyar makaranta muna masa addu’ar Allah ya kara sashi cikin zuciyar al-ummah.
Nan muka kawo kars nhen tattaunawar,Ku tara mako mai zuwa domin jin bakuwar ko bakon
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!