Connect with us

LABARAI

‘Sarakuna Na Da Muhimmiyar Gudunmawa Kan Rage Mutuwar Jarirai’

Published

on

An bukaci Sarakunan gargajiya da su kara himma domin tabbatar da rage yawan mutuwar kananan yara, da mata masu juna biyu a lokacin da suke nakuda a fadin jihar Bauchi.
Kwamishiniyar lafiya ta jihar Dakta Zuwaira Hassan Ibrahim ita ce ta mika wannan bukatar, a lokacin wani taron ganawa da Sarakunan gargajiya, wanda ma’aikatar lafiya da hadin guiwar hukumar lafiya tun daga matakin farko tare da asusun kulawa da kananan yara na majalisar dinkin duniya suka shirya shi, saboda zaburar da sarakunan dangane da kara bayar da ta su gudunmawar wajen, rage yawan mutuwar ta hanyar fadakarwa, da kuma ilmantar da al’ummarsu a kowane lokaci.
Ta ce, “Mun san cewar akwai abubuwan da ake yi; amma muna son mu ga wasu sababbi ne, wadanda za mu kawo da za su taimaka mana wajen wannan fadi tashin. Ku ne kuka fi kusantar jama’armu, ta yaya kuke gani za mu hada kai da ku, saboda mu gudu tare mu kuma tsira tare.
“Wannan dalilin ne ya sa muka kira ku saboda mu tattauna, mun san ku iyayenmu ne, kun fi mu da shekaru, kuma kun fi mu sanin matsalolin jama’armu kai tsaye, don haka idan muka hada shawarwarin mu da naku za a samu ci gaba, wajen rage yawan mutuwar kananan yara,” In ji kwamishiniyar.
Dokta Zuwaira Ibrahim Hassan ta kuma kara bayyana cewar daya daga cikin musabbabin yawan mutuwar yara, da ake samu yana faruwa ne a sakamakon kin zuwa awo a asibitoci, da mata ke yi tare da ma kin zuwa asibiti, lokacin haihuwa, saboda haka ne ta jawo hankalin iyaye maza da mata, da suke kauce ma wannan lamarin, tana mai shaida cewar ta hanyar haihuwa a asibiti ne, za a iya samun agajin gaggawa da mace mai juna biyu ke bukata, domin taimakwa mata da kuma abinda ke cikinta.
Jami’in kula da allurar rigakafin yau da kullum na jihar Bauchi, Dakta Jibril Umar Muhammad ya jaddada muhimmancin iyayen kasa kan rigakafin, inda ya ce “Shi ya sa muka ga ya dace mu kira iyayen kasa saboda su zaburar da jama’a, a duk lokacin aka haihu, muna son a yi rijistar abin da aka haifa a wannan unguwar, bayannan kuma a tura su asibiti domin su karbi rigakafi, saboda tsira daga cutattukan da suke jawo musu nakasa da mace-mace, musamman a farkon shekaru biyar na rayuwarsu,” in ji shi.
A jawabinsa, shugaban kwamitin Sarakuna kan fannin inganta kiwon lafiya na jihar Bauchi, Sarkin Dass, Alhaji Usman Bilyaminu Usman, ya bayyana cewar daya daga cikin abubuwan da suke hana mata zuwa asibiti shi ne, halin rashin kirki da wasu ma’aikatan kiwon lafiyar ke nunawa a bakin aikin su, don haka ne ya jawo hankalin ma’aikatan jinyar da su canza halayen su wanda a cewar sa, zai kawo saukin rashin halartar iyaye mata asibiti domin awo da kuma kula da lafiyarsu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!